An bani goron gayyatar koma wa APC - Ortom

An bani goron gayyatar koma wa APC - Ortom

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta bayyana bukatar zawarcin gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom, ta nemi ya yi wanka ya dawo cikinta yayin da babban zaben kasa na 2023 ya gabato.

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe, shi ne ya bayyana hakan da cewa jam’iyyar adawa a jiharsa, APC, ta kawo masa goron gayyata inda ta bayyana zawarcinsa da take yi.

Ortom ya sanar da hakan ne a ranar Asabar yayin wani babban taron jam’iyyar PDP da aka gudanar a filin wasanni na Aper Aku da ke Makurdi, babban birnin Benuwe.

Gwamnan ya ce bayan tuntuba da neman jin ta bakin wasu daga cikin makusantansa na jiki da kuma jam’iyyar PDP reshen jihar, ya yanke shawarar yin watsi da tayin.

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe
Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe
Asali: UGC

Ya ce zai sanar da shawarar da yanke ta kin karbar goron gayyatar barin jam’iyyar PDP ga sauran abokanansa a APC.

Ortom ya kuma tabbatar wa da magoyan baya cewa, da yardarm Ubangiji nasarar da jam’iyyar PDP ta samu a zaben 2019 za ta maimaita fifikon ta a zaben 2023.

Ya ce nasarorin da jam’iyyar ta samu a babban zaben kasa da ya gabata na da nasaba ne da goyon bayan da mambobinsu ke bai wa jam’iyyar.

A bangare guda Legit.ng ta ruwaito cewa, Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya mayarwa takwaransa na Kano, Abdullahi Ganduje martani mai zafi bayan ya ce babu wani abu 'a zo a gani' da ya yiwa al'ummar Edo.

Yayinda yake magana a fadar shugaban kasa ranar Juma'a, Ganduje wanda shine shugaban kwamitin yakin neman zaben APC a jihar Edo ya ce gazawar Obaseki zai saukaka musu wajen samun nasara a zaben ranar 19 ga Satumba.

Amma martani kan jawabin Ganduje, mai magana da yawun Obaseki, Crusoe Osagie , ya ce Ganduje bai da alhakin auna kokarin Obaseki saboda "irin bidiyon da ya bayyana kansa yana cusa Dalan da ya karba daga yan kwangila."

KARANTA KUMA: An nada Farfesa Sagir sabon shugaban jami'ar Bayero

Jawabin yace: "Maganar da gwamna Ganduje yayi kan kokarin Obaseki a ofis abin dariya ne.

Hakazalika abin kunya ne saboda APC ta gaza fahimtar abinda ake nufi da kokari saboda irin namijin kokarin da gwamna Obaseki yayi a bangarori daban-daban ya sanya soyayyarsa cikin zukatan mutan jihar Edo."

"Babu irin kananan maganganun da APC da masu yakin neman zabenta zasuyi da zai goge ayyukan da suka bazu a lunguna da sakon jihar Edo."

"Ganduje bai da hakkin auna kokarin gwamna Obaseki ko wani gwamna saboda yanada kashi a gindi, wanda yake bukatar wankewa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng