Buhari da Atiku sun aika sakon ta'aziya ga iyalan Isyaku Rabiu da Sanata Kashamu

Buhari da Atiku sun aika sakon ta'aziya ga iyalan Isyaku Rabiu da Sanata Kashamu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika sakon ta'aziyya ga iyalan Isyaku Rabiu, bisa rasuwar shahararren dan kasuwa a Kano, Alhaji Shehu Rabi’u, yayin da Atiku Abubakar ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayi Sanata Kashamu.

Da yake mika sakon ta'aziyyar kai tsaye ga iyalan Isyaku Rabiu da na Abdulsamad Rabiu, shugaban kamfanin BUA, wanda dan uwan mamacin ne, Buhari yace Alhaji Shehu ya bada taimako ga kasar ta fuskar kasuwanci da masana'antu.

Ya roki Allah ya ba iyalan mamacin juriyar wannan rashi, inda kuma shugaban kasar a madadin 'yan Nigeria ya ke yiwa masarautar Kano, gwamnatin jihar ta'aziyyar wannan rashi.

Garba Shehu, hadimin shugaban kasar ta fuskar watsa labarai, shine ya fitar da sakon ta shafinsa na Twitter, a ranar Alhamis, 8 ga watan Agusta, 2020.

KARANTA WANNAN: 'Chanja Buratai, Sadique, Ekwe Ibas, ba shi zai kawo karshen matsalar tsaro ba'

A wani labarin kuma, Bayan sanarwar mutuwar Sanata Buruji Kashamu, Atiku Abubakar, da Ben Murray-Bruce sun mika sakon ta'aziyyarsu ga iyalan mamacin.

Atiku Abubakar, wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP a zaben 2019, ya yi addu'ar Allah ya jikan mamacin, ya ba iyalansa hakurin rashinsa.

Sanata Buruji Kashamu (marigayi)
Sanata Buruji Kashamu (marigayi)
Asali: Depositphotos

A nashi sakon ta'aziyyar, tsohon sanata mai wakiltar mazabar Bayelsa ta Gabas a tsakanin 2015-2019, Ben Murray-Bruce ya bayyana mamacin a matsayin amininsa.

Murray-Bruce ya ce sau tari, bacci ne kadai ke rabasa da Sanata Kashamu, kuma ba zai taba mantawa da shi ba. Ya roki Allah ya ba iyalansa hakurin jure rashin da suka yi.

Atiku Abubakar da Ben Murray-Bruce sun mika sakon ta'aziyyar tasu ne a shafukansu na Twitter.

Rahotanni sun bayyana cewa, Sanata Kashamu ya mutu ne a ranar Asabar 8 ga watan Agusta a asibitin FCC da ke Lagos, bayan fama da rashin lafiya ta annobar COVID-19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel