'Yan sandan Bauchi sun azabtar da yarona har ya mutu, suka wurgar da gawarsa'

'Yan sandan Bauchi sun azabtar da yarona har ya mutu, suka wurgar da gawarsa'

- Hajara Ismail, ta yi ikirarin cewa 'yan sandan 'Township' a jihar Bauchi suka kashe mata yaronta bayan azabtar da shi

- Ko da aka tambayeta kan zarge zargen da ake yi na cewar yana sace sace, Hajara ta ce: "Karya suke yi masa wallahi."

- Ta bayyana cewa, DPO tare da wasu 'yan sanda guda shida cikin mota kirar Hilux ne suka kawo mata gawar yaron

Wata mata mai shekaru 53, Hajara Ismail, ta bayyana takaici da bacin ranta akan yadda 'yan sandan 'Township' a jihar Bauchi suka kashe mata yaronta bayan azabtar da shi.

Ta bayyana cewa sun kama yaron ne tare da wasu abokansa da zargin suna satar kajin wani jami'in 'yan sanda da yayi ritaya a garin.

A zantawarta da jaridar Punch, Hajara Ismail, mahaifiyar Ibrahim Kampanlala, ta labarta cewa a ranar Juma'a ne 'yan sandan suka kawo gawar Ibrahim gidan, ana tsakiyar bikin kanwarsa.

"A lokacin da suka zo, suna neman gidan, sai yara suka nuna masu, amma ni aka hana ni fitowa waje, na samu da kyar na fita waje don ganin abunda ke faruwa.

"A lokacin 'yan sandan suka fito da shi daga mota, suka wurgo shi kasa, har wuyansa ya karye, amma a rashin saninmu, ashe har ya mutu tun kafin wannan lokaci.

"DPO ya ce da ni, 'ga gawar yaronki nan; mun kamashi yana fashi da makami. Ba mune muka aikata hakan a kansa ba; muma haka muka same shi muka kawo maki shi'. A nan muka shigar da shi daki, a matacce."

Ta bayyana cewa, a lokacin da aka kawo mata gawar yaron, DPO na tare da wasu 'yan sanda guda shida cikin mota kirar Hilux, lokacin baya sanye da kakin 'yan sanda.

KARANTA WANNAN: Ka janye sunan Jonathan da Awolowo da ka sanyawa tashoshin layin dogo - Clark ga Buhari

'Yan sandan Bauchi sun azabtar da yarona har ya mutu, suka wurgar da gawarsa'
'Yan sandan Bauchi sun azabtar da yarona har ya mutu, suka wurgar da gawarsa'
Source: Twitter

Ko da aka tambayeta ko yaron nata yana alaka da masu aikata laifi ta amsa cewa: "A unguwarmu babu 'yan sara suka, ban ma san sun kama Ibrahim ba, gawarsa kawai na gani sun maido mun.

"Abokinsa Bala ne ya zo yake sanar da ni cewa suna aikin gini ne lokacin da 'yan sandan suka zo suka tafi da shi. Tabbas 'yan sanda ne suka aikata hakan akan dana, su suka kashe shi."

Ko da aka tambayeta kan zarge zargen da 'yan unguwar Doya suke yi na cewar yaron da abokansa biyu suna addabar unguwar na tsawon lokaci, Hajara ta ce: "Karya suke yi masa wallahi."

"Shi ba a nan ma yake aiki ba, yana zuwa hakar ma'adanai a Burga, ko yazo ganin gida baya wuce kwanaki uku yake komawa. Kuma da shirin zai koma bayan Sallar Lahya."

Da aka tambayeta abunda take bukata yanzu, ta bayyana cewa "Ko da na ce zan kaisu kara kotu bai da kudin yin haka. Yanzu haka rashin lafiya nake tunda suka kawo gawarsa.

"Abunda kawai zan sanarwa 'yan sandan shine da sun kawo mana shi a matsayin barawo ba gawarsa ba tunda sunce sata yayi. Me ya hana basu kaishi bursin ba idan gaskiya ne?

"Sun cuce ni, sai dai Allah ya saka mun, domin akwai ranar sakayya, akwai ranar da karfinsu ba zai yi tasiri ba, ranar da babu wani mai karfi sai Allah," a cewar Hajara Ismail.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel