Ka janye sunan Jonathan da Awolowo da ka sanyawa tashoshin layin dogo - Clark ga Buhari

Ka janye sunan Jonathan da Awolowo da ka sanyawa tashoshin layin dogo - Clark ga Buhari

Jagoran kabilar Ijaw, Chief Edwin Clark, a ranar Alhamis ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya janye sunayen tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da na Chief Obafemi Awowolo da ya sanyawa wasu tashoshin layin dogo na kasar.

Clark, a wata zantawa da manema labarai, ya bayyana karramar a matsayin "cin fuska", yana mai cewa Jonathan da Awolowo, sun cancanci fiye da hakan.

Ya bayyana cewa da yawan mutane da suka yi zamani da Awolowo sun samu karatun boko kyauta daga wajensa.

A cewarsa, cakuda mutanen da basu tsinana komai a ci gaban kasarsu da muhimman mutane irin Awolowo da Jonathan raini ne, kuma abun ayi tur.

"A yayin da ake cewa wai karramawa ce da gwamnatin tarayya ta yiwa tsohon shugaban kasar da ma'aikatarka, ta sufuri, domin mun san cewa tsohon shugaban kasar ne ya aza harsashin gina tashoshin layin dogon.

"Mu 'yan yankin Niger Delta da ma masu hankali daga 'yan Nigeria, mun yi Allah-Wadai da wannan karramawa, cin fuska ce a hada shi da wasu mutane marasa kishin kasa," a cewar Clark.

KARANTA WANNAN: 'Yajin aikin da mu ka shiga zai fara aiki da zarar an bude jami'o'i' - NASU da SSANU

Ka janye sunan Jonathan da Awolowo da ka sanyawa tashoshin layin dogo - Clark ga Buhari
Ka janye sunan Jonathan da Awolowo da ka sanyawa tashoshin layin dogo - Clark ga Buhari
Asali: UGC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta kaddamar da wani shafin yanar gizo wanda jama'a zasu rinka duba sakamakon zabe kai tsaye.

A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, mai magana da yawun INEC, Festus Okoye, ya ce shafin zai "karfafa gudanar da sahihin zabe wanda babu magudi a cikinsa."

Ya ce amfani da shafin zai fara ne daga zaben maye gurbi na dan majalisar Nasarawa ta tsakiya wanda kuma za ayi amfani da shi a zaben gwamnonin Edo da Ondo.

Sai dai, Okoye ya ce shafin bashi da alhakin tattara sakamakon zabe, don haka, za a ci gaba da tattara sakamakon zabe kamar yadda aka saba.

Tattara sakamakon zabe a zabukan da suka gabata ya zama babbar damuwa ga tsarin gudanar zaben Nigeria, wanda a karshe ke sa jam'iyyu suki amince da sakamakon zaben.

Ya ce INEC ta himmatu wajen magance duk wasu matsaloli da suka shafi demokaradiyyar zaben kasar, "lallai ya zama wajibi a kidaya kowacce kuri'a."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel