Rashin tsugunawa don bada zobe: Budurwa ta ki amincewa da bukatar aure (Bidiyo)

Rashin tsugunawa don bada zobe: Budurwa ta ki amincewa da bukatar aure (Bidiyo)

- Abubuwan mamaki basu taba karewa a duniya, kuma idan da ran ka za ka sha kallo

- Wani bidiyo da ke yawo a kafafaen sada zumuntar zamani ya janyo cece-kuce a tsakanin samari da 'yan mata

- A bidiyon, budurwar ta ki karbar zoben saurayin don amincewa da bukatar aurenta da yake saboda bai durkusa mata ba

Wani bidiyo a cikin kwanakin nan da ke yawo a kafafen sada zumuntar zamani ya bai wa jama'a mamaki.

A bidiyon, an ga mutumin yana mika bukatar auren budurwarsa a karkashin bishiya, amma sai ya sha mamakin da bai taba tsammani ba.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, mutumin na mika bukatar ne ta hanyar mika mata zobe yayin da dukkansu ke tsaye amma sai budurwar ta ki karba.

Ta bukaci saurayin da ya durkusa a kan guiwoyinsa yayin mika mata zoben.

Wani mutum wanda ake tsammanin shi ya nadi bidiyon da wayarsa, ya shawarci saurayin da ya gurfana a kan guiwoyinsa kamar yadda budurwar ta bukata, amma yace Allah ya kashe shi a take ba zai durkusa ba.

KU KARANTA: Jarumta: 'Yan kauye sun yi wa 'yan bindiga mugun duka, sun kashe daya a Katsina

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel