Da duminsa: INEC ta bude shafin yanar gizo da za a iya kallon sakamakon zabe kai tsaye

Da duminsa: INEC ta bude shafin yanar gizo da za a iya kallon sakamakon zabe kai tsaye

- Hukumar INEC ta bude shafin yanar gizo wanda jama'a zasu rinka duba sakamakon zabe kai tsaye

- Sai dai shafin bashi ba zai iya tattara sakamakon zabe ba, don haka, za a ci gaba da tattara sakamakon zabe a takardu

- Hukumar na fatan cewa wannan ci gaba zai sa a rinka gudanar da sahihin zabe, kuma hankulan al'umma ya kwanta

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta kaddamar da wani shafin yanar gizo wanda jama'a zasu rinka duba sakamakon zabe kai tsaye.

A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, mai magana da yawun INEC, Festus Okoye, ya ce shafin zai "karfafa gudanar da sahihin zabe wanda babu magudi a cikinsa."

Ya ce amfani da shafin zai fara ne daga zaben maye gurbi na dan majalisar Nasarawa ta tsakiya wanda kuma za ayi amfani da shi a zaben gwamnonin Edo da Ondo.

Sai dai, Okoye ya ce shafin bashi da alhakin tattara sakamakon zabe, don haka, za a ci gaba da tattara sakamakon zabe kamar yadda aka saba.

Tattara sakamakon zabe a zabukan da suka gabata ya zama babbar damuwa ga tsarin gudanar zaben Nigeria, wanda a karshe ke sa jam'iyyu suki amince da sakamakon zaben.

Ya ce INEC ta himmatu wajen magance duk wasu matsaloli da suka shafi demokaradiyyar zaben kasar, "lallai ya zama wajibi a kidaya kowacce kuri'a."

KARANTA WANNAN: Sai da jirgin ruwa ya kai tsakiyar teku ya dare gida biyu, mutane 9 sun mutu

Da duminsa: INEC ta bude shafin yanar gizo da za a iya kallon sakamakon zabe kai tsaye
Da duminsa: INEC ta bude shafin yanar gizo da za a iya kallon sakamakon zabe kai tsaye
Asali: UGC

"Domin bunkasa sahihancin zabenmu, hukumar ta yanke shawarar samar da shafi a yanar gizo, mai taken "SAKAMAKON ZABEN INEC KAI TSAYE (IReV).

"Shafin zai taimakawa 'yan Nigeria su rinka kallon adadin kuri'un da aka jefa a kowacce rumfar zabe a yayin da aka kidaya sakamakon zaben ranar," a cewar sanarwar.

"Hukumar na son sanar da jama'a cewa shafin ba shi da alhakin tattara sakamakon zabe. Za a ci gaba da tattara sakamakon zaben kamar yadda doka ta tanadar.

"Za a ci gaba da cike takardu da kaisu cibiyar tattara sakamakon zaben har zuwa lokacin bayyana sakamakon.

"Hukumar na fatan cewa wannan ci gaba zai sa a rinka gudanar da sahihin zabe, kuma hankulan al'umma ya kwanta, tunda suna kallon duk kuri'ar da za a kirga a rumfar zabe kai tsaye."

A yayin da hukumar ke shirin gudanar da zaben maye gurbi na Nasarawa a ranar Asabar, hukumar ta ce a karshen zaben, mutane zasu iya duba sakamakon zaben a shafinta na IReV.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel