Sai da jirgin ruwa ya kai tsakiyar teku ya dare gida biyu, mutane 9 sun mutu

Sai da jirgin ruwa ya kai tsakiyar teku ya dare gida biyu, mutane 9 sun mutu

- Akalla mutane tara ne ake sa ran sun rasa rayukansu bayan da wani jirgin ruwa ya dare gida biyu a jihar Sokoto

- Ana kyautata a cewa hatsarin ya faru ne sakamakon mutane 30 da ke akan jirgin ruwan, wanda nauyinsu ya wuce kima

- Shugaban karamar hukumar Goronyo ya umurci Sarakunan Ruwa na yankin da su rinka hana jirgi shiga rafin idan har an lura da akwai hadari

Akalla mutane tara ne ake sa ran sun rasa rayukansu bayan da wani jirgin ruwa ya dare gida biyu a tsakiyar teku a Birjingo, karamar hukumar Goronyo, jihar Sokoto.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mafi akasarin wadanda hatsarin ya rutsa da su mata ne da kananun yara, har da wata budurwa da ake daf da aurenta, da kuma mahaifiyarta.

Rahotanni sun bayyana cewa mutane 30 ne akan jirgin ruwan a lokacin da hatsarin ya afku.

An ruwaito cewa fasinjojin na kan hanyarsu ta zuwa gonar shinkafa da ke tsallaken rafin, inda suke aikatau a gonar.

Ya yin da yake tabbatar da faruwar lamarin, kansilan gundumar Birjingo, Isa Muhammad, ya ce hatsarin ya faru da misalin karfe 8 na safiyar Laraba.

KARANTA WANNAN: Kwaminitin gwamnonin Arewa maso Gabas sun fara ganawa a Maiduguri

Sai da jirgin ruwa ya kai tsakiyar teku ya dare gida biyu, mutane 9 sun mutu
Sai da jirgin ruwa ya kai tsakiyar teku ya dare gida biyu, mutane 9 sun mutu
Asali: Twitter

Sarkin garin Birjingo, Alhaji Shehu Dangaladima, ya ce jirgin ruwan ya dare gida biyu ne sakamakon nauyin da aka yi masa.

Shugaban karamar hukumar Goronyo, Zakari Muhammad Shinaka, ya ce, "a sa'ilin da muka ji labarin hatsarin, mun tara wadanda suka iya ruwa mutum 50, inda suka yi nasarar ceto wasu da ransu."

A cewarsa, zuwa yanzu an gano gawar mutane bakwai a yayin da ake ci gaba da neman gawar mutane biyu.

Shinaka, wanda ya jajantawa iyalan wadanda hatsarin ya rutsa da su, ya kuma bukaci Sarakunan Ruwa na yankin da su rika hana yin lodin mutane masu yawa a cikin jirgin ruwa.

"Ka ku bar wani jirgin ruwan da ke dauke da mutane da yawa tsallaka rafinku, musamman idan aka fahimci akwai hadari, kar ma abar jirgin ya shiga ruwa," Shinaka ya bada umurni.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel