Rundunar sojin Nigeria ta sa hannu kan jarjejeniyar fara sarrafa kayan aikinta da kanta

Rundunar sojin Nigeria ta sa hannu kan jarjejeniyar fara sarrafa kayan aikinta da kanta

- Rundunar sojin Nigeriata sa hannu kan wata takardar jarjejeniya ta fara sarrafa kayayyakin aikin da rundunar sojin take bukata

- A baya rundunar ta sarrafa wasu ababen hawa masu kariyar EMRAP, motocin sintiri na TYP, da takalma, hulunan kwano da sauransu

- Da wannan ci gaban, Nigeria za ta rage kudaden da take kashewa wajen sayo da kayyakin da rundunar soji ke bukata

Rundunar sojin Nigeria a ranar Alhamis, ta sa hannu kan wata takardar jarjejeniya da kamfanin Super Green Security, da hukumar masana'antun tsaro ta Nigeria da kuma cibiyar injiniyoyi.

Ta kulla wannan yarjejeniyar ne domin fara sarrafa kayayyakin aikin da rundunar sojin take bukata da ma na fannin tsaron kasar baki daya.

Kulla yarjejeniyar na karkashin umurnin shugaban Buhari na 5 da aka sa a dokar 2018, da nufin bunkasa sarrafa kayan aiki ta hanyar amfani da ilimin kimiya da fasahar injiniyoyin kasar.

Idan za a tuna, a kokarin gwamnatin tarayya na tabbatar da cewa kowanne mutum ko kungiya sun sarrafa kayan aikinsu da kansu, rundunar sojin ta dauri damarar cimma hakan.

KARANTA WANNAN: Yan majalisa 17 na jihar Edo sun tsige kakakin majalisasu

A baya rundunar ta sarrafa wasu ababen hawa na yaki da take amfani da su a matsayin ababen hawa masu kariyar EMRAP, motocin sintiri na TYP, da takalma, hulunan kwano da sauransu.

Wakilin hafsan rundunar sojin a wajen sa hannun shine, Lt Gen LO Adeosun, shugaban sashen tsare tsare na rundunar.

Wakilin kamfanin SGSN da kuma shugaban cibiyar ED sune Manjo Janar AB Abubakar (rtd) da Manjo Janar SS Araoye.

Babban shugaban hukumar masana'antun tsaro na kasa, Manjo Janar Victor Ezugwu yayin sanya hannu akan takardar ya jinjinawa shugabancin rundunar sojin na mayar da rundunar sojin kasar ta rinka sarrafa kayayyakin aikinta da kanta.

A cewar M.J Victor Ezuwgu wannan kokari na TY Buratai zai ragewa kasar kudaden da take kashewa wajen sayowa rundunar sojin kayayyakin da take amfani da su.

Hotunan sa hannu kan takardar yarjejeniyar:

Rundunar sojin Nigeria ta sa hannu kan jarjejeniyar fara sarrafa kayan aikinta da kanta
Rundunar sojin Nigeria ta sa hannu kan jarjejeniyar fara sarrafa kayan aikinta da kanta
Asali: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel