Da duminsa: Yan majalisa 17 na jihar Edo sun tsige kakakin majalisasu

Da duminsa: Yan majalisa 17 na jihar Edo sun tsige kakakin majalisasu

Yan majalisu 17 na majalisar dokokin jihar Edo, da suka hada da mambobi 14 da a baya aka bayyana kujerarsu a matsayin wofi, sun yi ikirarin cewa sun tsige kakakin majalisar jihar, Francis Okiye, da mataimakinsa, Roland Asoro.

Sun yanke wannan hukuncin ne a ranar Alhamis a wani boyayyen wuri a Benin City, babban birnin jihar, awanni bayan da jami'an tsaro suka mamaye zauren majalisar.

A bangarensu, sunce sun nada Victor Edoror, mai wakiltar mazabar Esan ta tsakiya, da Emmanuel Agabje, daga mazabar Akoko-Edo II a matsayin kakakin majalisar da mataimakinsa.

A wajen taron, 'yan majalisu 14 da aka zabe su, an rantsar da su tare da sauran 'yan majalisun 3 wadanda suka yi mubayi'a ga Osagie Ize-Iyamu na jam'iyyar APC, suka ce sun tsige kakakin.

Majalisar dokokin jihar Edo ta kasance cikin rikici tun a shekarar 2019, wacce ta sake rikicewa a yanzu a yayin da ake shirye shiryen zaben gwamnan jihar.

KARANTA WANNAN: Gwamnan Bauchi ya nada hadima mai kula da harkokin zawarawa

Da duminsa: Yan majalisa 17 na jihar Edo sun tsige kakakin majalisasu
Da duminsa: Yan majalisa 17 na jihar Edo sun tsige kakakin majalisasu
Asali: Depositphotos

An zabi 'yan majalisu 24 daga mazabu 24 na jihar a babban zaben 2019. Sai dai, 10 daga cikinsu, an rantsar da su ne a ranar 17 ga watan Yulin shekarar, lamarin da ya jawo zaune-tsaye.

Biyar daga cikin 10 na 'yan majalisun an rantsar da su tare da mataimakin kakakin majalisar na wancan lokacin, Yekini Idiaye, kuma sun yi mubayi'a ga Ize Iyamu a makon da ya wuce.

Wannan lamarin ya faru ne bayan da suka zargi gwamnan jihar Godwin Obaseki da mayar da majalisar dokokin jihar ba a bakin komai ba.

Domin daukar mataki a hannunsu, a ranar Laraba, 'yan majalisun hudu cikin biyar, suka taru suka tsige Idiaye, tare da maye gurbinsa da Asoro.

Amma 'yan majalisun da ke goyon bayan Ize-Iyamu sun yi ikirarin cewa su sun tsige shi tare kakakin majalisar jihar, Okiye.

Cikakken labarin yana zuwa...

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel