Yanzu-yanzu: An sako masu zanga-zangar juyin juya hali da aka kama a Abuja
Shugabancin babban birnin tarayya Abuja ta sako masu zanga-zanga 40 da aka kama a Unity Fountain a kan zarginsa da ake da take dokar dakile yaduwar korona.
An kama masu zanga-zangar ne a Unity Fountain inda suke zanga-zangar juyin juya hali ta RevolutionNow.
Amma kuma Mai shari'a Idayat Akanni, wacce ke yanke hukunci a kotun tafi da gidanka bata samu yin zaman kotun ba.
A yayin jawabi a madadin kwamitin tabbatar da dokar korona na ministan, Kwamared Ikharo Attah, ya ce za su iya zanga-zangarsu amma kuma masu tabbatar da an bi doka sai sun yi aikinsu.
Ya ce, wadanda suke zanga-zangar sun take dokar kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasar da ta gindaya dokar nesa-nesa da juna tare da saka takunkumin fuska.
Kamar yadda yace: "A kalla mun saki mutane 40 da muka kama kuma mun bukacesu da su kiyaye dokokin dakile yaduwar korona a duk lokacin da za su yi zanga-zanga.
"Suna da damar yin zanga-zangar tare da fadin abinda ke ransu amma dole ne su kiyaye dokoki kuma."

Asali: Twitter
KU KARANTA: Rashin takunkumi: Hotunan jami'an tsaro na lalata da budurwar da suka kama a cikin mota
A wani labari na daban, da safiyar yau, Laraba, ne jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) suka kama Olawale Bakare da wasu sauran mutane shida da ke sanye da huluna ruwan dorawa a yayin da su ka fito gudanar da zanga-zangar juyin juya hali.
Jami'an DSS sun kama matasan ne a yankin Olaiya da ke Osogbo, babban birnin jihar Osun. Matasan a karkashin jagorancin Bakare sun yi tattaki zuwa ofishin 'yan jarida domin gabatar da jawabi a kan zanga-zangar da su ka fara.
A yayin da matasan su ke jira a gaban ofishin 'yan jaridar domin a yi mu su iso, sai wasu 'yan sanda su ka tunkarosu tare da fara tattaunawa dasu.
A yayin da su ke tattaunawa ne sai ga wasu jami'an tsaron na hukumar DSS sun dira a wurin tare da yin awon gaba da matasan.
Kazalika, jami'an rundunar 'yan sanda sun tarwatsa matasan da su ka fito zanga-zangar juyin juya hali da safiyar ranar Laraba a yankin Ikeja.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng