Obaseki ya musanta zargin bayar da kwangiloli ta hanyar da ba ta dace ba

Obaseki ya musanta zargin bayar da kwangiloli ta hanyar da ba ta dace ba

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, ya musanta zargin da ake masa na cewa yana amfani da wani kamfaninsa mai suna Afrinvest Limited wajen tatse lalitar dukiyar al’ummar.

Ana dai zargin gwamnan da cewa yana yin abinda ake kira ‘cinye du’ ta hanyar bai wa kamfanin da ya mallaka duk wata kwangilar aiki ta gwamnatinsa.

Sai dai gwamnan ya musanta wannan zargi cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Crusoe Osagie, ya fitar yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai a ranar Talata cikin birnin Benin.

Osagie ce wannan zargi da ake yi ba wani abu bane face sharri wanda jam'iyyar APC ke kulla wa da nufin bata sunan gwamnan.

Ya kara da cewa, wannan wani tuggu da aka kulla domin ganin an janye hankalin ubangidansa daga zaben gwamnan jihar da ya gabato kuma hakan ba zai yi tasiri ba.

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo
Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo
Asali: UGC

An ruwaito cewa, wasu daga cikin mambobin jam’iyyar PDP karkashin wata kungiya ta masu ruwa da tsaki, sun mika wa hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta ICPC korafi a kan gwamnan.

'Ya'yan jam'iyyar sun nemi hukumar da ta binciki Gwamna Obaseki a kan zarginsa da laifin yin ruf da cikin kan kudaden al’umma.

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa, Andrew Egboigbe, wani mamba a jam'iyyar PDP a mazaba ta uku ta karamar hukumar Orhionmwon, ne ya mika korafin ga hukumar ICPC a ranar Litinin.

"A matsayinmu na 'yan jihar Edo masu kishi, bamu da inda za mu kira gida da ya wuce jihar Edo.

“Muna mika korafin nan a kan gwamnan jiharmu da kamfaninsa na Afrinvest Ltd.”

KARANTA KUMA: Gwamnan Fintiri ya kaddamar da aikin gadar sama ta N8.8 a jihar Adamawa

“Wannan ya biyo bayan mun gano cewa gwamnan yana amfani da kujerarsa wurin bai wa kamfaninsa kwangiloli da ayyukan ci gaban kuma yana wadaka da kudin ta hanyar da ba ta dace ba,” inji Egboigbe.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Gwamna Obaseki, ya ja kunnen 'yan siyasa da ke shirin tada zaune tsaye a jihar da su sauya tunani ko kuma su girbi duk abinda suka shuka.

A wata tattaunawa da aka yi da Obaseki, wanda shine dan takarar zaben gwamna a jihar Edo karkashin jam'iyyar PDP, ya jaddada cewa a shirye yake ya damke duk wanda zai tada hankali a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel