'Dalibai sun kauracewa makarantu yayin da aka koma a jihar Benuwe

'Dalibai sun kauracewa makarantu yayin da aka koma a jihar Benuwe

'Dalibai ‘yan kalilan ne su koma aji a jihar Benuwe yayin da aka buɗe makarantu a ranar Talata sakamakon fargabar annobar korona da har yanzu ta mamaye zukatan iyaye.

Manema labarai da suka kai ziyara wasu makarantu a birnin Makurɗi, sun lura cewa mafi rinjayen kaso na ɗalibai sun kauracewa makarantun, yayin da aka samu ‘yan kalilan ne suka koma.

A wata makarantar Sakandire ta Mount Saint Gabriel, manema labarai sun riske ta tsaf-tsaf kuma an tanadi ruwan wanke hannu da sabulu da kuma sunadarin tsaftace hannu (sanitizer) a wurare daban-daban a cikinta.

Haka kuma dukkanin mutanen da ke cikinta suna sanye da takunkumin rufe fuska kamar yadda jaridar daily Trust ta ruwaito.

Shugaban makarantar, Rabaran John Asen, ya ba da shaidar cewa, daga cikin dalibai 300 ‘yan aji uku da ‘yan aji shida da ake tsammanin dawowarsu, wadanda suka dawo basu wuce dari ba.

Yadda ake feshin magani a cikin aji
Hoto daga jaridar Daily Trust
Yadda ake feshin magani a cikin aji Hoto daga jaridar Daily Trust
Asali: Twitter

“Mun yi wa gaba daya makarantar feshin magani kuma mun tanadi sunadarin tsaftace hannu kamar yadda aka shata a ka’idodin dakile bazuwar cutar korona.”

“Sai an yi wa kowane dalibi gwaji tun a bakin kofa kafin ya shigo makaranta.”

“Mun kiyaye duk wasu ka’idodi da gwamnati da kuma hukumomin lafiya suka shar’anta.”

Haka kuma a wata Makarantar Gwamnati ta Makurdi da manema labarai suka kai ziyara, babu alamar gyara na share-share ko yanke ciyayi a yayin da ma’aikata da dama sun hallara a cikinta.

Shugabar makarantar, Agnes Land, ta ce dukkanin ma’aikata 130 da makarantar take da su sun dawo aiki, amma dalibai biyu ne kacal suka dawo cikin 193 da ake tsammanin dawowarsu.

Ta ce daliban da suka dawo sun kasance daga cikin dalibai 43 ‘yan aji shida da ake tsammanin dawowarsu domin kamala shirye-shiryen zana jarabawa.

“Sai dai ban yi mamaki ba a yayin da makarantar ba ta kan tsari iri guda da sauran makarantu na ragowar jihohin Arewa 18, inji Agnes.

“Daliban biyu da suka dawo mazauna jihar Benuwe ne kuma akwai malaman da suka yi musu darasi kafin su koma gida.”

“Sai dai har yanzu ba mu yi makarantar feshin magani ba amma mun kiyaye duk wasu sharuda da gwamnati ta shata mana.

“Amma tabbas za mu yi kokari mu yi feshin magani a makarantar kafin dalibai su karasa dawowa.

KARANTA KUMA: 2023: Tanko Yakassai, Mbazulike Amechi sun goyi bayan shugabancin kabilar Ibo

A wata makaranta ta Government Model School, shugaban makarantar ya ce sun dauki nauyin feshin magani ba tare da jiran gwamnati ba.

Uswan Godwin yayin bayyyana farin ciki dangane da yadda dalibai dama suka dawo, ya ce an kuma kiyaye dokar bayar da tazara da nesa-nesa da juna a cikin kowane aji.

Ya ce an yi amfani da na’urar daukan dumin jikin dukkanin dalibai tun kafin shigowarsu cikin makaranta.

Sai wani dalibin makarantar da manema labarai suka nemi jin ta bakinsa, y ace an umarci da su taho da takunkumin rufe fuska guda biyu-biyu da kuma sunadarin tsaftace hannu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel