Ba sani ba sabo: Hukuncin da za ayiwa duk dan wasan da yayi tari a filin kwallo

Ba sani ba sabo: Hukuncin da za ayiwa duk dan wasan da yayi tari a filin kwallo

Yan wasa suyi hattara, domin kuwa za su iya samun jan kati daga alkalin wasa ma damar suka yi tari da gangan a fuskar wani dan wasan ko jami'an wasa. Kungiyar kwallon kafa ta turai tayi nuni da cewa cin fuskane yin tari ana tsakiyar annobar COVID-19.

Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta kasa da kasa (IFAB) ta ce ya ragewa alkalin wasan ya tantance ko anyi tarin don cin zarafi ko kuma ba da gan gan aka yi ba.

IFAB ta ayyana yin tari da gangan ga wani dan wasa a matsayin "cin zarafi, zagi ko amfani da kalaman batanci ko motsi mai nuna rashin da'a".

"Kamar yadda yake ga kowanne laifi, dole alkalin wasane zai yanke hukunci akan gaskiyar dalilin yin tarin," a cewar ta.

"Idan har ba da gangan bane, to alkalin wasa ba zai dauki mataki akan tarin da aka yi a tazara mai nisa tsakanin yan wasan ba.

"Amma idan har ta tabbata anyi tarin ne domin cin mutunci, to a nan alkalin wasa zai iya daukar mataki."

Kundin tsarin dokokin laifuka da hukunce hukunce na kwallon kafa a turai zai fara aiki nan take da zaran wani dan wasa ya karya doka.

KARANTA WANNAN: Ku koma gona kada yunwa ta kashe ku - Tambuwal ya shawarci mutan Sokoto

Ba sani ba sabo: Hukuncin da za ayiwa duk dan wasan da yayi tari a filin kwallo
Ba sani ba sabo: Hukuncin da za ayiwa duk dan wasan da yayi tari a filin kwallo
Asali: Twitter

Kundin tsarin dokokin laifuka da hukunce hukunce na kwallon kafa a turai zai fara aiki nan take da zaran wani dant wasa ya karya doka.

"Idan laifin bai munana ba da har za a bayar da jan kati, to za a bada katin gargadi na aikata laifi. Amma idan har laifin ya munana, to hukuncin jan kati ne kawai," a cewar IFAB.

Ta kara da cewa kada alkalan wasa su rinka yin hukunci akan tarin da aka saba gani, sai dai akan tarin da aka tabbatar anyi shine domin cin fuskar wani dan wasa ko jami'i.

A wani labarin; Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto, ya roki manoma da su ci gaba da kara kaimi wajen yin noma domin taimakawa kasar wajen farfado da tattalin arzikinta.

Ya ce hakan ne zai sa abinci ya wadatu da gudun mace mace saboda yunwa.

Tambuwal ya bayyana hakan a jihar Sokoto, yana mai nuni da cewa tattalin arzikin kasar na ci gaba da tabarbarewa, fiye da tunanin mutane.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel