Dandanon budurcinta nayi - Dan achaba da ya yi lalata da diyar cikinsa

Dandanon budurcinta nayi - Dan achaba da ya yi lalata da diyar cikinsa

Kotu ta musamman ta cin zarafi da ke Ikeja a jihar Legas a ranar Talata, ta yankewa wani dan achaba mai shekaru 37 hukuncin shekaru 20 a gidan yari sakamakon lalata diyarsa mai shekaru 12 da yayi.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, Mai shari'a Sybil Nwaka, yayin yankewa Emmanuel Idoko hukunci, ya ce masu gabatar da karar sun bada shaidu kwarara.

An kama dan achaba Idoko da laifin saka yatsansa a gaban diyarsa.

Alkalin yace: "an kama wanda ake zargin da cin zarafi tare da lalata wanda ya ci karo da sashi na 261 na dokokin laifukan jihar Legas.

"A don haka aka yanke masa hukuncin shekaru 20 a gidan gyaran hali."

Babajide Boye ne dan sandan da ya gabatar da kara, kuma ya sanar da kotun cewa Idoko ya yi laifin ne tsakanin watan Yuli zuwa Nuwamba na 2017 a gidansa da ke Oworoshoki, jihar Legas.

"Ya lalata diyarsa mai shekaru 12 ta hanyar tura yatsansa cikin gabanta," Boye yace.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, shaidu hudu kwarara ne suka tabbatar da aukuwar lamarin yayin da Idoko ya ki amsa laifinsa.

A ranar 5 ga watan Maris na 2019, Dr Oyedeji Alagbe, wanda likita ne a Mirabel Centre, ya ce yarinyar ta tabbatar masa da aukuwar lamarin kuma ya dubata tare da tabbatar da hakan.

Alagbe ya ce: "Ta tabbatar da cewa suna zama tare da 'yan uwanta maza ne tare da mahaifinsu duk da basu tare da mahaifiyarsu.

"Ta fara fuskantar matsalar ne tun a shekarar 2016, kafin a tura ta Mirabel Centre.

"Ta ce mahaifinta ya zo gida inda yace ya ji ana cewa ba budurwa bace, kuma yana bukatar gane gaskiyar lamarin.

"Ya tirsasata tayi tsirara sannan ya yi amfani da yatsansa ya saka a a gabanta. Ya bukaci amfani da mazakutarsa don gwajin amma ta ki amincewa, lamarin da yasa yayi mata duka tare da azabtar da ita."

Dandanon budurcinta nayi - Dan achaba da ya yi lalata da diyar cikinsa
Dandanon budurcinta nayi - Dan achaba da ya yi lalata da diyar cikinsa. Hoto daga ThisDay
Asali: Twitter

KU KARANTA: Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai hari sansanin 'yan gudun hijra, sun kashe rayuka 16

Idoko ya musanta cewa ya ga tsiraicin diyarsa da kuma saka hannu a gabanta don gwajin budurci.

"Diyata na bin kawayen banza, makwabtana suna fadin abubuwa da yawa a kanta. Da farko ban yarda ba har sai da na gani da idona.

"A ranar 21 ga watan Nuwamban 2017, na ga diyata da wasu yara maza yayin da dan uwanta ke cikin gida yana kallon talabijin.

"A lokacin da na kirata sai yaran suka gudu kuma ta ki sanar da ni waye saurayinta a cikinsu.

"A lokacin da nayi kokarin dukanta, ta yi kokarin ramawa kamar yadda ta ga kawayenta na yi wa iyayensu. Hakan ce ta sa nayi mata mugun duka a ranar," yace.

A lokacin da aka mika masa bayanin da yayi wa 'yan sanda na cewa ya ga tsiraicin diyarsa, Idoko ya sanar da kotun cewa kayanta ne suka cire a yayin da yake ladabtar da ita.

"Ban yaga mata kaya ba. Ban fahimta ba a lokacin da na sanar da hakan har aka rubuta," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel