Samari 3 sun mutu a hatsarin tsakar dare

Samari 3 sun mutu a hatsarin tsakar dare

Matasa uku; Unuayefe Wenena, Miracle Alex, da Sofia Agido, sun yi gamo da ajali a wani mummunar hatsarin mota da ya auku tsakar dare a ranar Lahadi.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan lamari ya auku ne a kan titin Amukpe zuwa Igbeku da ke garin Sapele a jihar Delta.

An ruwaito cewa wata mota kirar Toyota Corolla da take tafe a sukwane wadda mamatan ke ciki, ta gwabza wa wata babbar motar daukan siminti da ke tsaye.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, nan take matasan uku suka riga mu gidan gaskiya bayan motar da suke ciki ta dake bayan Tirelar da ke tsaye.

Sufeto Janar na 'yan sanda
Sufeto Janar na 'yan sanda
Asali: Twitter

Wata majiya ta bayyana cewa, matasan wanda babu wanda ya haura shekaru 18 a cikinsu, ajali ya katse musu hanzari a kan hanyarsu ta dawo wa daga gidan rawa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Delta ya tabbatar da aukuwar wannan lamari yayin zantawa da manema labarai a ranar Talata.

Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar da ke kiyaye aukuwar hadurra ta kasa FRSC, ta sanar da cewa, an yi hatsarurruka daban-daban har kashi 3,947 yayin da kuma aka samu mace-macen mutane 1,758 da suka biyo baya.

Jami’in hulda da al’umma na hukumar, Bisi Kazeem, shi ne ya sanar da hakan yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa a birnin Abuja.

KARANTA KUMA: Bashin N5m ya sa ɗan kasuwa zai kashe kansa a Legas

Mista Kazeem ya ce an samu aukuwar wannan hatsarirrika a tituna daban-daban da ke fadin kasar a tsakanin watan Janairu zuwa Maris na shekarar da muke ciki.

Ya ce hatsarirrika 3,947 ne suka auku cikin watanni ukun farko na shekarar 2020, wanda ya hadar da motoci 6,448, kuma aka samu salwantar rayukan mutane 1,758 yayin da kuma mutum 11,250 suka jikkata.

A cewarsa an samu mafi girman kaso na wannan ibtila’i a shiyyar Kaduna sai kuma shiyyar Enugu da ta biyo baya a mataki na biyu.

A sanadiyar haka ne Mista Kazeem yake shawartar direbobi a kan yi wa dokokin tuki biyayya da kuma bayar da hadin kai ga jami’an da ke rage cunkoso a kan tituna.

Ya kuma shawarci fasinjoji da su bincike lafiyar ababen hawa yadda ya kamata kafin shiga saboda galibi motocin da ake haya da sub a su cancanci hawa titi ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel