Bashin N5m ya sa ɗan kasuwa zai kashe kansa a Legas

Bashin N5m ya sa ɗan kasuwa zai kashe kansa a Legas

Jami’an ’yan sandan jihar Legas sun kubutar da wani mutum mai suna Abiodun Adeyinka, da yayi yunkurin jefa kansa cikin wani kudiddinfi sakamakon bashin N5m da yayi masa katutu.

Jami’in hulda da al’umma na hukumar ’yan sandan jihar, Bala Elkana, shi ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai.

Ya ba da rahoton cewa “Jami’an ’yan sanda dake sintiri a kan gadar Third Mainland kan titin Abaraje na yankin Ikotun, sun ceto wani bawan Allah da yake yunkurin jefa kansa cikin halaka”.

Inda ya kara da cewa “lamarin ya auku ne ranar juma’a 31 ga watan yulin 2020 da misalin 1:50 na rana, inda daga bisani jami’an suka rankaya da shi zuwa ofishin ’yan sanda dake Bariga domin gabatar da bincike akansa”.

Jami'an 'Yan sanda
Hoto daga jaridar Premium Times
Jami'an 'Yan sanda Hoto daga jaridar Premium Times
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, sakamakon gagarumar asara da Mista Abiodun ya tafka ya sanya ya kasa biyan bashin kudaden da ya ranto daga bankin Microfinance domin bunkasa kasuwancinsa.

Jaridar ta kara da cewa, halin rashin iya biyan kudaden ya sanya mutumin mai shekaru 45 ya hau dokin zuciya inda ya nufi gadar ta Third Mainland domin sawwake kansa a cikin kudiddifin.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Jigawa, ta sanar da cewa a cikin watanni shidan da suka gabata, an samu mafi ƙarancin masu laifi a jihar idan an kwatanta da watannin baya.

Rundunar 'yan sandan ta alakanta nasarorin da ta samu na ƙarancin masu aikata laifuka cikin a sakamakon inganta dabarun dakile aukuwar miyagun laifuka a jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Abdul Jinjiri, shi ne ya sanar da hakan a ranar Talata yayin hira da kamfanin dillancin labarai na kasa a Dutse, babban birnin jihar.

KARANTA KUMA: Hukumar WAEC ta fitar da jadawalin jarrabawar 2020

SP Jinjiri ya ce an samu kararraki 35 na laifukan fyade a tsakanin watan Janairu zuwa Yunin shekarar da muke ciki, wanda shi ne adadi mafi yawa cikin kididdigar alkaluman aikata laifuka.

Babban jami'in ya ce fashi da makami shi ne na biyu ta fuskar yawan laifukan da aka aikata yayin da a halin yanzu akwai mutane 21 da suka shiga hannu kan zargin laifin fashi da makami.

Mista Jinjiri ya ce an samu kararraki 18 na laifukan kisan gilla da kuma kararraki 5 na laifukan garkuwa da mutane, yayin da kuma aka samu kararraki 13 na wasu laifukan na daban da basu saba aukuwa ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel