Wanke kai: NDDC ta gayyaci Buhari ya bude wani babban aikinta da yaci N24bn a Bayelsa

Wanke kai: NDDC ta gayyaci Buhari ya bude wani babban aikinta da yaci N24bn a Bayelsa

- Hukumar NDDC ta gayyaci shugaba Buhari da ya sa albarka ta hanyar bude aikin titi mai kilomita 29 daga Ogbia zuwa Nembe a jihar Bayelsa

- Hanyar ta kawo sauki wajen hada garin Yenagoa da babban garin Nembe a karon farko, kuma ta rage tsawon tafiya zuwa Yenagoa daga awa 3 zuwa daya da rabi

- Tuni dai majalisar tarayyar ta bukaci a rushe kwamitin sa ido na hukumar tare da mayar da hukumar NDDC karkashin umurnin shugaban kasa

Hukumar bunkasa yankin Niger Delta NDDC ta gayyaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sa albarka ta hanyar bude aikin titi mai kilomita 29 daga Ogbia zuwa Nembe a jihar Bayelsa.

Hukumar, a cikin wata sanarwa a ranar Talata, mai taken 'NDDC ta gayyaci shugaba Buhari bude aiki', ta ce aikin, wanda ya ratsa garuruwa 14 zai ci kudi har naira biliyan 24.

Sanarwar dauke da sa hannun daraktan harkokin huldodi, Charles Odili, a Abuja, ta ce titin an ginashi ne bisa hadin guiwar hukumar da kamfanin mai na Shell.

Kuma hanyar ta kawo sauki wajen hada garin Yenagoa da babban garin Nembe a karon farko.

Odili yace, "Domin cimma aiki mai nagarta, sai da aka fara hako tabo na tsawon mita hudu, tare da cike ramin da yashi domin nagartar titin.

"Titin ya rage doguwar tafiya zuwa Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, daga awanni uku zuwa awa daya da rabi.

"Aikin ba wai yana nuna kokarin NDDC ba ne ba kadai, sai dai samar da kyakkyawar alaka tsakanin hukumar da kamfanonin mai na kasa da kasa wajen gina yankin."

KARANTA WANNAN: Magance matsalar tsaro: Buhari ya bada umurnin yin garambawul a rundunonin tsaro

Wanke kai: NDDC ta gayyaci Buhari ya bude wani babban aikinta da yaci N24bn a Bayelsa
Wanke kai: NDDC ta gayyaci Buhari ya bude wani babban aikinta da yaci N24bn a Bayelsa
Asali: Twitter

Hukumar NDDC da kumar ma'aikatar da ke kula da harkokinta sun kasance cikin takun saka da majalisar tarayya kan zarge zargen cin hanci da rashawa da sace biliyoyin kudade.

A watan da ya gabata shugaban ma'aikatar NDDC, Godswill Akpabio da shugaban hukumar NDDC, Kemebradikumo Pondei, sun amsa tambayoyin gaban kwamitin bincike na majalisar.

A yayin binciken ne, ministan ya fasa kwai, inda ya bayyana cewa ko a cikin 'yan majalisun, akwai wadanda ke cin moriyar kudaden hukumar NDDC.

Da ya ke tsokaci kan sunayen 'yan majalisun da Akpabio ya saki, Odili ya ce, "Kwmaitin sa ido na hukumar sun gamsu da sunayen da tuni ke hannun masu binciken kudi.

"Ba wai sunayen sun fito daga hannun Akpabio bane, sun fito daga hannun NDDC ne. Sunayen na cikin takardu 8,000 da tuni aka turawa masu binciken kudi don yin nazari akansu.

"Kada haifaffun yankin Niger Delta da sunayensu ke a takardun suji tsoro, domin hukumar ta san anyi amfani da su ne wajen karbar kwangiloli, kuma bincike zai fitar da gaskiyar hakan.

"Manufar fitar da sunayen shine tona asirin shuwagabannin kwamitoci na majalisar tarayyar da ke bin hanyoyi wajen karbar kwangila daga hukumar, da yawansu ba a hukunta su ba."

Tuni dai majalisar tarayyar ta bukaci a rushe kwamitin sa ido na hukumar tare da mayar da hukumar NDDC karkashin umurnin shugaban kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel