Cikin watanni 6 an samu mafi ƙarancin masu laifi a jihar Jigawa - Rundunar 'Yan sanda
Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Jigawa, ta sanar da cewa a cikin watanni shidan da suka gabata, an samu mafi ƙarancin masu laifi a jihar idan an kwatanta da watannin baya.
Rundunar 'yan sandan ta alakanta nasarorin da ta samu na ƙarancin masu aikata laifuka cikin a sakamakon inganta dabarun dakile aukuwar miyagun laifuka a jihar.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Abdul Jinjiri, shi ne ya sanar da hakan a ranar Talata yayin hira da kamfanin dillancin labarai na kasa a Dutse, babban birnin jihar.
SP Jinjiri ya ce an samu kararraki 35 na laifukan fyade a tsakanin watan Janairu zuwa Yunin shekarar da muke ciki, wanda shi ne adadi mafi yawa cikin kididdigar alkaluman aikata laifuka.

Asali: Twitter
Babban jami'in ya ce fashi da makami shi ne na biyu ta fuskar yawan laifukan da aka aikata yayin da a halin yanzu akwai mutane 21 da suka shiga hannu kan zargin laifin fashi da makami.
Mista Jinjiri ya ce an samu kararraki 18 na laifukan kisan gilla da kuma kararraki 5 na laifukan garkuwa da mutane, yayin da kuma aka samu kararraki 13 na wasu laifukan na daban da basu saba aukuwa ba.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, rundunar 'yan sandan jihar Jigawa a bara ta karbi kararraki 61 na fyade, 32 na fashi da makami, 52 na kisan gilla, 4 na garkuwa da mutane dai kuma 13 na sauran laifuka.
Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta damke wani mutum mai shekaru 38, Adeshina Abdulazizi, a kan laifin yi wa yarinya mai shekaru 3 fyade a Unguwar Inyamurai da ke kwaryar birnin Bauchi.
KARANTA KUMA: Gwamnoni za su gana da shugaban kasa game da rashin tsaro
A wata takarda da kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Ahmed Mohammed Wakili ya sa hannu, ya ce, "A ranar 2 ga watan Augustan 2020, wanda ake zargin ya ja karamar yarinyar cikin dakinsa inda yayi mata fyade sannan kuma aka kama shi a take."
Takardar ta bayyana cewa, wanda ake zargin ya amsa laifinsa inda ya shaida cewa ya yi wa kananan yara a kalla hudu fyade.
Matsalar fyade tana ci wa jama'a tuwo a kwarya a fadin Najeriya baki daya.
Lamarin da ya sanya majalisun jiha suka fara nazari kan ta'adar fyade tare da kirkiro dokoki masu tsauri don magance wannan matsalar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng