Za a buɗe makarantun Kano a ranar 10 ga watan Agusta

Za a buɗe makarantun Kano a ranar 10 ga watan Agusta

Gwamnatin Kano ta yanke shawarar amincewa da buɗe makarantun jihar a ranar 10 ga watan Agusta.

Muhammad Sanusi Kiru, kwamihsinan ilimi, shi ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai a ranar Litinin, 3 ga watan Agusta.

Kwamishinan ya kuma umarci dukkan shugabannin makarantu da su fara shirye-shirye karbar ɗaliban makarantun kwana 'yan ajin shida a ranar 9 ga Agusta, yayin da na 'yan jeka-ka-dawo za su koma a ranar 10 ga watan Agusta.

An iyakance buɗe makarantun ga ɗaliban da ke ajin karshe masu shirye-shiryen zana jarrabawar kammala karatun sakandire.

"Lallai ne duk cibiyoyin ilimi su bi ka'idojin da aka shimfida domin sake buɗe makarantun" inji kwamishinan.

Gwamnan Kano; Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan Kano; Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

Ya kuma kara da cewa, ma'aikatar muhalli tare da hadin gwiwar takwarorinta na ilimi, sun fara yi wa makarantu feshin magani a shirye-shiryen da ake gudanarwa domin komawa ɗalibai.

A sakamakon bullar annobar korona, gwamnatin tarayya tun a watan Maris ta ba da umarnin rufe kafatanin makarantu a fadin kasar.

Daga bisani bayan shafe watanni hudu gwamnatin tarayya ta bada damar buɗe makarantu ga ɗaliban da suke ajin karshe a matakin sakandare.

Gwamnatin yayin bayar da wannan dama, ta kuma nemi makarantun da su tabbatar da ka'idojin da ma'aikatar ilimi ta gindaya domin dakile yaduwar cutar ta korona.

Hukuncin wanda ya gabata a ranar 27 ga watan wuli a wata tattaunawa ta musamman ta gudana tsakanin ma'aikatar ilimi da kwamishinonin ilimi na jihohi 36 da ke fadin tarayya.

Sauran wadanda gwamnatin ta tuntuba sun hadar da; kungiyar malamai ta najeriya, mambobin makarantu masu zaman kansu da manyan shuwagabannin bangarorin jarrabawa.

A yau Talata ne za a buɗe duk makarantun sakandire na gwamnatin tarayya 104 kamar yadda karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ya ba da sanarwa.

KARANTA KUMA: Mutane na iya yada wa kuliyoyi da karnuka cutar korona

Ministan ya ba da sanarwar hakan ne a ranar Litinin, 3 ga watan Agusta, yayin da ya kammala tattaunawa da kwamishinonin ilimi na jihohi 36 da ke fadin tarayya da kuma sauran masu ruwa da tsaki.

Cikin sanarwar da mai magana da yawun ma'aikatar ilimi ta tarayya, Ben Goong ya sanya wa hannu, ya yabi shugabannin makarantun dangane da tabbatar duk wani shiri na komawar ɗalibai a ranar Talata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng