Ganduje ya amince a bude cibiyoyin jarabawar JAMB masarautu 5 na Kano

Ganduje ya amince a bude cibiyoyin jarabawar JAMB masarautu 5 na Kano

- Gwamnatin jihar Kano ta amince da bude cibiyoyin zana jarabawar JAMB a masarautu biyar na jihar

- Gwamnatin za ta kafa majalisar jiha kan watsa labarai da sadarwa (ICT) domin yada ilimin ICT tun daga kauyuka

- Sannan akwai yiyuwar gwamnatin za ta yi amfani da tsohon kamfanin buga jarida na Triump ta bude kasuwar 'yan canji ta zamani

Gwamnatin jihar Kano ta amince da bude cibiyoyin zana jarabawar JAMB a masarautu biyar na jihar da suka mamaye kananan hukumomi 44 na shiyyoyi 5 na jihar.

Kwamishinan watsa labarai, Malam Muhammadu Garba ya bayyana hakan jim kadan bayan fitowa daga taron majalisar zartaswa na jihar da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar.

"An yanke shawarar kara adadin cibiyoyin zana jarabawar ne la'akari da korafe korafen da al'ummar ke shigarwa, na tura daliban jihar zuwa jihohin Bauchi, Kaduna, Jigawa ko Katsina."

Mallam Garba ya kuma bayyana cewa a yayin wannan zaman, majalisar zartaswar ta amince da bude cibiyar jiha kan watsa labarai da sadarwa (ICT) domin yada ilimin ICT tun daga kauyuka.

"Majalisar za ta kasance karkashin kwamishinan kimiyya da fasaha da kirkira da kuma na kananan hukumomi.

KARANTA WANNAN: Shuwagabannin tsaro basu da wa'adin ajiye mulki, Buhari ne kawai zai iya tsige su

Ganduje ya amince a bude cibiyoyin jarabawar JAMB masarautu 5 na Kano
Ganduje ya amince a bude cibiyoyin jarabawar JAMB masarautu 5 na Kano
Asali: Twitter

"Yayin da kwamishinonin watsa labarai, ilimi, manyan makarantu da shuwagabannin kananan hukumomi 44 za su zamo mambobi," a cewarsa.

Kwamishinan ya bayyana cewa majalisar ta karbi wata bukata daga wani mai kirkira akan ayi amfani da tsohon kamfanin buga jarida na Triump a bude kasuwar 'yan canji ta zamani.

Kasuwar za ta kasance ta farko a Nigeria, da kuma wata bukata daga kamfanin kadarori na Fari, inda ya bukaci a bunkasa otel din Daula da aka yi watsi da shi, ya koma rukunin gidaje.

Kwamishinan ya bayyana cewa majalisar ta kuma karbi bukatar gina babban kantin sayar da kaya a harabar otel din Daula.

Malam Garba ya tariyo wata bukata makamanciyar wannan da malajisar ta karba a makon da ya gabata daga kamfanin Mudatex da a gina babban kantin sayayya a otel din Daula.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel