Mayakan IS sun dira kurkukun Afghanistan, sun saki daruruwan fursunoni

Mayakan IS sun dira kurkukun Afghanistan, sun saki daruruwan fursunoni

Fiye da fursunoni 300 ne suka ranta a na kare bayan sun bazama a ranar Litinin, a yayin da mayakan kungiyar ta'adda ta ISIS suka kai kari wani gidan yari a kasar Afghanistan kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Hakan ya faru ne a yayin ake ci gaba da ruguntsumi tsakanin fursunoni da jami'an tsaro a gidan cin sarka.

Harin ya fara aukuwa ne tun a daren ranar Lahadi a kurkukun da ke Gabashin garin Jalalabad, inda akalla rayukan mutum 29 sun salwanta yayin da kuma fiye da mutane 50 suka jikkata.

Mai magana da yawun gwamnan lardin Nangarhar, Attaullah Khugyani, shi ne ya sanar da hakan kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Daga cikin fursunoni 1,793, sama da 1,025 ne suka yi kokarin tserewa kuma aka sake kama su yayin da 430 suka rage a cikin gidan yarin.

Kurkukun Afghanistan da mayakan IS suka kai hari
Kurkukun Afghanistan da mayakan IS suka kai hari
Asali: Twitter

Ya ce fararen hula, fursunoni da kuma jami'an tsaro na cikin wadanda rayukansu suka salwanta.

Khugyani ya ce an kashe 'yan bindiga takwas yayin da jami'an tsaro suke mayar da martani ga maharan.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wani mutum dan kasar Birtaniya da ake zargi da fyade da kashe wata abokiyarsa ya shaidawa kotu cewa ta mutu ne sakamakon "tsautsayi da aka samu lokacin da suke saduwa".

An bukaci mutumin, Wesley Streete, mai shekaru 20, ya raka yarinyar, Keeley Bunker zuwa gidanta ne bayan sun dawo daga gidan casu da daddare tare da wani abokinsu a birnin Birmingham.

A ranar 19 ga watan Satumban shekarar 2019 ne Bunker ya bayyana cewa ya jefa gawar ta a wani kududufi da ke kusa da su kuma ya rufe da rassan bishiya kamar yadda ya shaidawa kotu.

Kawun yarinyar ya gano gawar ta yayin da suke bincike a Wigginton Park da ke Tamworth, Staffordshire kimanin nisan kilomita 23 arewa maso gabashin Birmingham.

Da ya ke kare kansa a gaban kotu a karo na farko, Streete ya bayyana abinda ya yi ikirarin ya faru kafin mutuwar ta.

KARANTA KUMA: Masu cutar korona a Najeriya sun kai 43,841 - NCDC

Ya amince da cewa tabbas sun tafi Kulob tare a birnin Birmingham tare da Bunker da wata Monique Riggon kafin daga baya suka koma gidansu da Tamworth.

Su uku suka isa gidan Riggon amma Bunker ta ce tana son ta tafi gidan ta ta kwana a gadonta hakan yasa aka ce Streete ya yi mata rakiya.

Ya yi ikirarin cewa sun fara hirar masoya a hanya sannan suka sumbaci juna kana suka yi lalata a Wigginton Park.

"Na shake mata wuya a lokacin da muke lalata kuma tsautsayi yasa ta mutu," in ji shi.

Ya amsa cewa ya yi wa iyalanta da abokansa da yan sanda karya game da abinda ya faru saboda yana jin kunyar halin da ta mutu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel