Ku kare kanku daga harin makiyaya da na 'yan daban daji - Kaigama ya shawarci 'yan Najeriya

Ku kare kanku daga harin makiyaya da na 'yan daban daji - Kaigama ya shawarci 'yan Najeriya

Matsin lamba na hare-haren 'yan fashi da makiyaya ya janyo wani babban limamin addini ya shawaraci al'ummar Najeriya su dauki matakin kare kai a hannunsu.

Babban limamin cocin katolika ta Abuja, Rabaran Ignatius Kaigama, ya kirayi masu fadi aji na kasar da su mike tsaye wajen kare al'umma daga hare-haren 'yan ta'adda da ke ci gaba da tsananta a kasar.

Rabaran Ignatius ya yi wannan kira da a tashi a kare kai muddin gwamnati ta gaza kare al'umma daga hare-haren makiyaya da na 'yan daban daji.

Doriya a kan hakan kuma fiye da komai, babban limamin ya roki gwamnati ta kara zage dantse wajen bai wa al'ummar kasar nan kariya daga hare-haren masu tayar da zaune tsaye.

Ignatius Kaigama da Buhari
Ignatius Kaigama da Buhari
Asali: UGC

Kaigama wanda a karshen mako ya yi furucin hakan yayin ganawa da manema labarai a Abuja yayin bikin murnar cikarsa shekaru 62.

Ya dora laifin tashin hankalin al'umma da rashin tsaro da ke addabar kasar kan rashin adalci.

Ya ce kashe bil Adama ta'addanci ne mai girma kuma abin takaici ne yadda kashe-kashe ya zama ruwan dare a kasar nan.

Babban limamin ya kuma bayyana damuwa dangane da yadda gwamnati ta gaza kawo karshen cin hanci da rashawa a kasar nan, inda ya yi kira ga kan sauya fasalin hukumomi masu yaki da rashawa domin inganta ayyukansu.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Hukumar jirgin kasa ta Najeriya ta rasa kudaden shiga har sama da naira biliyan daya tsakanin watan Maris da Agustan wannan shekarar.

Hakan ya biyo bayan dakatar da harkokin jirgin kasa mai safarar fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna da kuma Lagas zuwa Ijoko/Kajola da kuma jiragen kasa masu jigilar kayayyaki zuwa wurare mai nisa daga Lagas zuwa Kano.

KARANTA KUMA: Rauni game da shirye-shirye na barazana ga komawar ɗalibai a wannan mako

A halin yanzu na Abuja zuwa Kaduna sun fara aiki a ranar Laraba sannan an kara kudin da kusan sama da kaso 100%.

Binciken jaridar Leadership ya nuna cewa jirgin Abuja zuwa Kaduna na samar da naira 6,890,000 a kullun da yawan fasinjoji 4,000, inda masu karamin karfi ke biyan akalla 1,300.

Gaba daya tana tara kimanin naira miliyan 50 duk sati da kuma naira miliyan 200 duk wata daga jigilar da take yi daga Abuja zuwa Kaduna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng