Dalilin da yasa Gemade da su Dogara suka koma APC - Mr Yekini Nabena
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa jam'iyyar APC ta yi tsokaci kan dawowar Sanata Barnabas Gemade da tsohon kakakin majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara jam'iyyar.
APC ta ce dawowar kusoshin ya faru ne bayan maslaha da aka samu tsakanin 'yan jam'iyyar karkashin kwamitin riko na Mai Mala Buni na jihar Yobe.
Mataimakin mai magana da yawun jam'iyyar na kasa, Mr Yekini Nabena, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Abuja a ranar Lahadi.
Ya ce: "Dawowar Sanata Barnabas Gemade jam'iyyar APC wata alama ce ta nasarar da aka samu na dinke barakar jam'iyyar karkashin kwamitin Gwamna Mai Mala Buni.
"Gwamna Mai Mala Buni shine shugaban riko na jam'iyyar na kasa kuma shugaban kwamitin tsare tsare na musamman na jam'iyyar.
"Sanata Gemade, wanda shine tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, ya kasance cikin dandazon mutanen da suka koma APC, ciki kuwa har da Rt. Hon. Yakubu Dogara."
KARANTA WANNAN: Bauchi 2023: Dogara zai yiwa Gwamna Bala Abdulkadir ritaya daga siyasa | Legit TV Hausa

Asali: Twitter
A cewarsa, kwamitin shugabanci na jam'iyyar karkashin Gwamna Buni ya kawo karshen rikicin cikin gida na jam'iyyar tare da dawo da martabar jam'iyyar a idon wadanda sukayi fushi da ita.
"Muna bata tabbacin ci gaba mai amfani, duk wanda ya fice daga jam'iyyar saboda bacin rai, to ya dawo mu hada hannu wajen cimma muradun bunkasa al'ummar Nigeria baki daya.
"Abun jin dadi ne yadda kusoshin jam'iyyar da suke ganin martabar shugaban kasa Muhammadu Buhari suka ci gaba da goyawa kwamitin shugabancin jam'iyyar baya domin samar da maslaha.
"Muna kira ga magoya baya, mambobi, da kuma shuwagabanni da su ci gaba da taimakawa kwamitin rikon wajen magance matsaloli da rikice rikicen cikin jam'iyyar.
"Babban aikin zamar da jam'iyyar a matsayin tsintsiya madaurinki daya, ba aikin mutum daya bane, aikin kowa da kowa ne," a cewar kakakin jam'iyyar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng