Atiku ya bukaci Buhari da APC su nemi afuwar ‘yan kasa kan nauyin bashin da suka dora wa Najeriya

Atiku ya bukaci Buhari da APC su nemi afuwar ‘yan kasa kan nauyin bashin da suka dora wa Najeriya

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya kirayi shugaba Muhammadu Buhari da kuma jam'iyyar APC, a kan su bai wa 'yan Najeriya hakuri saboda nauyin bashin da suka tara wa kasar.

Atiku ya ce kamata ya yi gwamnatin Buhari ta amince da laifin cewa jefa kasar nan cikin katutu na bashi mai nauyin gaske.

Furucin tsohon mataimakin shugaban kasar ya zo ne a yayin da ake muhawara dangane da koma bayan ci gaba da kasar nan za ta fuskanta sakamakon kantar bashi.

Atiku ya ce, “Najeriya na da jimillar bashin ketare na dala biliyan 7.02 a ranar 29 ga Mayun 2015. A yau, bashinmu na kasashen waje ya kai dala biliyan 23 kuma yana ci gaba da karuwa."

Tsohon mataimakin shugaban kasa; Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban kasa; Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Sai dai jam'iyyar APC yayin mayar da martani, ta ce tsohon mataimakin shugaban kasar ba ya da cancantar shigar da wannan bukata.

Jam'iyyar APC ta bakin kakakinta Yekini Nabena, ta ce Atiku shi ne ya cancanci ya bai wa 'yan Najeriya hakuri kan basussukan da ya karbo a bankuna kuma har yanzu ya gaza biya.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wata kungiya mai yaki da rashin gaskiya, SERAP, ta maka gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a kotu kan gazawarta na yin bayani game da bashin da ta ke karbowa.

Wannan kungiya ta SERAP ta na so gwamnatin tarayya ta rika yi wa ‘Yan Najeriya bayani dalla-dalla game da kudin da ta aro daga kasar waje tun daga lokacin da ta karbi mulki.

KARANTA KUMA: Harin bom ya kashe mata da miji a Borno

SERAP ta fitar da jawabi a shafinta na Twitter ta na cewa: “Mun bukaci babban kotun tarayya da ke garin Abuja ta tursasawa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi cikakken bayani game da bashin kudin da gwamnatin ta karbo tun daga Mayun 2015.”

Kungiyar ta na son sanin ruwan da bashin da wannan gwamnati ta ke karbowa su ke dauke da su.

Haka kuma ta nemi sanin adadin kudin da Najeriya ta aro da yadda aka kashe su.

A wannan kara mai lamba ta FHC/ABJ/CS/785/2020 da aka shigar a gaban kotu a makon jiya, SERAP ta nemi Alkali ya umarci gwamnatin APC ta bayyana sharudan bashin da ta karbo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng