Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai hari sansanin 'yan gudun hijra, sun kashe rayuka 16

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai hari sansanin 'yan gudun hijra, sun kashe rayuka 16

Mayakan kungiyar ta'addanci na Boko Haram sun kashe a kalla rayuka 16 a wani hari da suka kai sansanin 'yan gudun hijira da ke arewacin kasar Kamaru, wani jami'i ya sanar.

"A halin yanzu yawan wadanda suka rasu sun kai 16, har yanzu ba a tabbatar da cewa ko Boko Haram bace da alhakin harin ba," wani shugaba mai suna Mahamat Chetima Abba ya sanar da AFP bayan harin tsakar dare da aka kai wa sansanin Nguetchewe.

Wani dan siyasa da ke yankin ya kwatanta jama'ar wurin da irin mutanen da ke boyewa idan maharan Boko Haram sun bayyana.

Kungiyar 'yan ta'addan da ta samo asali daga yankin arewa maso gabas na Najeriya tun 2009 ta saba kai hari tun a 2014, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Suna kan kai hari wurare da dama don satar dabbobi da kayayyakin abinci.

"A makonni kadan da suka gabata, an samu zaman lafiya amma daga baya sun yi amfani da ilimin sanin hanyar idan suka tsallake jami'an tsaro. Sun bamu mamaki," shugaban ya kara da cewa.

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai hari sansanin 'yan gudun hijara, sun kashe rayuka 16
Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kai hari sansanin 'yan gudun hijara, sun kashe rayuka 16. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kyawawan hotunan 'ya'ya mata na Bashir El-Rufai, dan uwan gwamnan Kaduna

A wani labari na daban, Sanata Ali Ndume, shugaban kwamitin majalisar dattawa a kan harkokin sojojin kasar nan, ya soki yadda ake karbar tubabbun Boko Haram tare da mayar da su cikin jama'a.

A makon da ya gabata, hukumar sojin Najeriya ta sako tubabbun 'yan ta'addan Boko Haram 601 bayan sun kammala shirin wayar musu da kai bayan sun tuba, wanda rundunar Operation Safe Corridor ke shiryawa.

A wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa a ranar Laraba, 29 ga watan Yuli, Ndume wanda ke wakiltar mazabar Borno ta Kudun, ya ce jama'arsa basu amince da gyaran hali da ake wa tubabbun 'yan Boko Haram ba.

Kamar yadda yace, mayakan ta'addancin ba za su taba sauya miyagun halayensu ba kuma ba za su tuba ba.

A yayin caccakar shirin, Ndume ya ce "Jama'ata basu amince da wannan shirin ba. Abinda ya fi shine a bar shi kawai.

"Ba wai hakuri suke bai wa jama'a ba, gwamnati suke bai wa hakuri tare da tunanin cewa sun gaza. Daga nan ake karbarsu tare da tarairayarsu," yace.

Ya kara da cewa, "Da yawa daga cikin wadanda suka tuban, guduwa suke yi su koma. Gwamnatin ta san abun yi kawai. Bai kamata a sake kawo maka wanda ya kashe maka iyaye ba ko 'yan uwa.

"Idan akwai gaskiya a cikin al'amarin, wadanda ke sansanin 'yan gudun hijara ne ya kamata a horar wurin sana'a ta yadda za su fara sabuwar rayuwa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel