Fashewar Bam ya kashe yara shida a Burkina Faso

Fashewar Bam ya kashe yara shida a Burkina Faso

Akalla mutane shida wanda akasarinsu yara ne sun mutu a yayin da wani bam ya tashi a Arewacin kasar Burkina Faso kamar yadda jami'an tsaro suka sanar a ranar Lahadi.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, bam din ya tashi ne a yayin da al'umma ke dawo daga hada-hadar yau da kullum a ranar Asabar wanda kuma ya janyo jikkatar wasu mutum hudu.

Babu shakka Arewacin kasar Burkina Faso ya shahara a matsayin yankin da 'yan ta'adda ke kai hare-hare wanda tun daga shekarar 2015 kawo yanzu, fiye da rayuka 1,000 sun salwanta yayin da kuma akalla mutum miliyan daya sun tarwatse daga matsugunansu.

Mutanen da fashewar bam din ya ritsa da su galibi kananan yara ne a yayin da suka kan hanyarsu ta dawo daga kiwo kamar yadda wani jami'i birnin Ouahigouya ya bayyana.

Hare haren bama-baman sun ci ga ninkuwa tun daga shekarar 2018, inda akalla rayukan dakarun soji da na farar hula 200 sun salwanta kamar yadda alkaluman kamfanin dillancin labarai na AFP suka nuna.

Fashewar Bam ya kashe yara shida a Burkina Faso
Fashewar Bam ya kashe yara shida a Burkina Faso
Asali: UGC

Ire-iren wannan hare-hare na aukuwa ne ta hanyar tarar hanzari da yi wa wadanda basu ji ba kuma basu gani ba kwanton bauna.

Masu tayar da kayar bayar sun kashe akalla mutum 4,000 a Mali, Nijar da kuma Burkina Faso kamar yadda alkaluman majalisar dinkin duniya suka nuna.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Gwamnan jihar Borno, Babagan Zulum, ya yi ikirarin cewa lallai akwai masu barna da gangan da ke aiki domin hana kawo karshen yaki da Boko Haram a Najeriya.

Channels TV ta ruwaito cewa Zulum ya yi zargin ne a Borno a ranar Lahadi, 2 ga watan Agusta, lokacin da ya hadu da takwarorinsa na jihar Kebbi, Atiku Bagudu da na jihar Jigawa, Badaru Abubakar.

KARANTA KUMA: Dakaru sun kubutar da mutane 17 daga hannun 'yan daban daji a Arewa maso Yamma

Zulum ya ce ya yarda akwai wasu runduna da ke aiki domin hana gwamnati kawo karshen ta’addanci a yankin arewa maso gabas.

Gwamnonin arewan biyu sun kai masa ziyara ne biyo bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai wa jerin motocinsa kwanan nan.

Taron ya kuma samu halartan tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima, Sanata Ali Ndume da mambobin majalisar dokokin jihar.

Gwamna Zulum ya ce akwai bukatar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya duba tsarin tsaron kasar da kyau domin tabbatar da ganin cewa kokarinsa bai tashi a banza ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel