Dakaru sun kubutar da mutane 17 daga hannun 'yan daban daji a Arewa maso Yamma
Rayukan 'yan daban daji 80 sun salwanta a yayin da rundanar dakarun sojin kasan Najeriya ta ke ci gaba da tsananta aikin kakkabe masu tayar da kayar baya a Arewa maso Yammacin Najeriya.
Rundunar sojin kasan Najeriya ta sanar da cewa ta samu nasarar cafke 'yan daban daji 33 yayin da kuma ta kwato shanu 943 da tumaki 633 gami da muggan makamai a yayin ci gaba da yakar 'yan ta'adda a jihar Katsina.
Haka kuma rundunar sojin a karkashin gudanarwar Operation Sahel Sanity, ta samu nasarar ceto mutane 17 da suka fada tarkon garkuwa ta 'yan daban daji yayin da kuma tartawatsa sansaninsu a yankin na Arewa maso Yamma.

Asali: Depositphotos
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin mukaddashin kakakin rundunar tsaro na kasa; Birgediya Janar Benard Onyeuko cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 2 ga watan Agusta.
Birgediya Janar Onyeuko ya ce bajintar da dakaru ke nuna wa wajen kakkabe miyagu ya sa manoma da 'yan kasuwa sun koma kan harkokinsu cikin aminci ba tare da wata fargaba ba a yankunan.
A cewarsa, shugaban hafsan sojin kasan Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, shi ne ya kaddamar da aikin dakaru na Operation Sahel Sanity a ranar 6 ga watan Yuli domin kara inganci kan ayyukan ganin bayan 'yan ta'adda.
KARANTA KUMA: Watan Yuli: Matukiyar jirgin yaki ta farko, abokanan Buhari, tsofaffin ministoci da sauran mashahuran mutane da suka mutu a Najeriya
Ya ce makasudin wannan sabon aiki wanda doriya ne a kan gudanarwar dakaru ta Operation Hadarin Daji, shi ne kawo karshen ta'addancin 'yan daban daji, barayin shanu, masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka a yankin na Arewa maso Yamma.
Kafin yanzu, wannan ayyuka na tayar da zaune tsaye da 'yan ta'adda ke yi ya janyo koma baya a fannin noma, zamantakewa da kuma sauran harkokin kasuwanci na al'umma a yankin.
Dakarun sojojin na Oeratiopn Sahel Sanity, sun gudanar da jerin ayyukan kakkabe 'yan ta'adda ta hanyar kai simame da aiwatar da sintiri a yankunan jihohin Sakkwato, Katsina da kuma Zamfara.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng