Watan Yuli: Matukiyar jirgin yaki ta farko, abokanan Buhari, tsofaffin ministoci da sauran mashahuran mutane da suka mutu a Najeriya
Watan Yulin 2020 zai ci gaba da kasancewa sananne a zukatan wasu daga cikin iyalai da 'yan uwan akalla mashahuran mutane 13 da mai yankan kauna ta yiwa lullubi a cikinsa.
Cikin kwanaki 31 da watan Yuli ya kunsa, Najeriya ta yi rashin matukiyar jirgin yaki ta farko a kasar, Tolutope Arotile da kuma na hannun daman shugaban kasa Muhammadu Buhari; Mallam Isa Funtua.
Haka kuma Najeriya ta yi babban rashi na wasu tsaffin ministoci; Sam Momah da Abdulganiyu AbdulRazaq.
A watan Yulin dai, ajali ya katse hanzarin wasu kusoshin gwamnati, manyan 'yan jarida da kuma jiga-jigan jam'iyyu daban-daban.
A yayin da wasunsu sun mutu ne a sakamakon cutar korona, wasu kuma wasu cututtukan na daban ne sanadiyar ajalinsu. Arotile ce kadai ta bakuncin lahira a sakamakon hatsarin mota.
Jaridar Premium Times ta yi nazari kan wasu takaitattun bayanai kan mashahuran mutanen da suka kwanta dama cikin watan Yuli kamar haka:
Shugaban Ma'aikatan fadar gwamnatin Jihar Borno

Asali: Facebook
Babagana Wakil, shi ne shugaban ma'aikatan fadar gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, wanda mai yankan kauna ta katsewa hanzari a ranar 1 ga watan Yuli.
Ana zargin mutuwarsa na da nasaba da cutar hawan jini da kuma gyambon ciki wato ulcer wadda ya yi fama da su na wani dan lokaci takaitacce.
Kwamishinan Lafiya na jihar Borno
Kwamishinan lafiya na jihar Borno, Wahab Adegbenro, ya mutu ne a ranar Alhamis, 2 ga watan Yuli.
Majiyoyin rahoto daga fadar gwamnatin jihar sun labarta cewa, kwamishinan ya yi gamo da ajali a gadon asibitin zana na jihar inda ya yi jinya.
Tsohon Jigo na jam'iyyar APC
A ranar 6 ga watan Yuli ne tsohon mataimakin shugaban am'iyyar APC na kasa, Inuwa Abdulqadir, ya ido biyu da ajali.
Marigayi Inuwa ya bar duniya bayan ya sha fama da wata 'yar gajeruwar rashin lafiya, inda ya yi jinya a asibitin koyarwa na Jami'ar Usman Danfodiyo da ke brinin Shehu.
Shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Kwara
Aminu Adisa Logun, shi ne shugaban ma'aikatan fadar gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara wanda cutar korona ta zame masa sanadiyar ajali a ranar 7 ga watan Yuli.
'Dan Majalisar Dokokin jihar Kwara
A ranar 10 ga watan Yuli ne dan majalisar mai wakiltar mazabar Kosofe a majalisar dookokin jihar Legas, Tunde Braimoh, ya kicibus da ajali bayan wata 'yar takaitacciyar rashin lafiya
Matukiyar jirgin yaki ta farko a Najeriya

Asali: Twitter
Rundunar dakarun sojin saman Najeriya NAF, a ranar 15 ga watan Yuli, ta sanar da mutuwar Tolutope Arotile, mace ta farko a Najeriya mai tuka jirgin yaki mai saukar ungulu.
Arotile mai shekaru 24 kacal a duniya, ta kwanta dama a sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya auku a Kaduna wanda ya gadar mata da munanan raunuka.
Aminin Shugaba kasa Muhammadu Buhari

Asali: Twitter
A ranar 20 ga watan Yuli ne wani na hannun daman shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mallam Isa Funtua, fada tarkon mai yankan kauna.
Marigayi Isa wanda tsohon minista ne a jamhuriya ta biyu, ya yi gamo da ajali ne a sakamakon bugun zuciya kamar yadda iyalansa suka bayyana.
Mai watsa labarai na gidan Rediyon Max FM
A ranar 24 ga watan Yuli, wata shahararriyar mai gabatar da rahotanni a gidan Rediyon Max FM da ke jihar Legas, Emmanuella Adepoju, ta yi gamo da karshenta bayan ta yi wata rashin mai nasaba da ciwon zuciya.
Tsohon minista kuma mahaifin gwamnan jihar Kwara
Ganiyu Folorunsho Abdulrazaq, mahaifin gwamnan jihar Kwara na yanzu, AbdulRahman Abdulrazaq, ya rasu a ranar 25 ga watan Yuli
Margayi Ganiyu ya kasance tsohon ministan kula da jiragen kasa a jamhuriyya ta farko. Ya bar duniya yana da shekaru 93 a duniya.
Ya rasu ya bar matarsa mai shekaru 92, Raliat AbdulRazaq da kuma 'ya'ya da jikoki.
Shugaban jam'iyyar PDP
A ranar 28 ga watan Yuli ne mai yankan kauna ta ziyarci shugaban jam'iyyar PDP na jihar Abiya, Johnson Onuigbo.
Rahotanni sun bayyana cewa, Johnson ya mutu ne a gadon cibiyar lafiya ta tarayya da ke birnin Umuahia.
Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha
Bayan ya yi murnar bikin cikarsa shekaru 77 a duniya a ranar 6 ga watan Yuli, cutar ciwon suga ta sanadiyar ajalin tsohon ministan kimiya da fasaha, Sam Momah, a ranar 29 ga watan Yuli.
Shugaban kabilar Yarbawa ta Afenifere
Ayorinde Fasanmi, shugaban kungiyar kabilar Yarabawa ta Afenifere, ya gamo da karshensa a ranar 30 ga watan Yuli, bayan ya yi fama da wata 'yar takaitacciyar rashin lafiya.
Marigayi Fasanmi yayin rayuwarsa ya kasance tsohon dan majalisar wakilar ta tarayya a jamhuriyya ta farko da kuma dan majalisar dattawa a jamhuriyya ta biyu.
Wani dan jarida na jihar Ogun
A ranar 30 ga watan Yuli ne mai yankan kauna ta katse hanzarin wani fitaccen dan jarida na gidan Rediyon Cowrie FM da ke birnin Abeokuta na jihar Ogun, Willy Thomas.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng