Bukukuwan Sallah: Yadda mata 7 suka mutu a gidan kitso

Bukukuwan Sallah: Yadda mata 7 suka mutu a gidan kitso

- Akalla mata bakwai ne suka mutu a wani shagon kitso a karamar hukumar Rijau da ke jihar Nigeri

- Ana hasashen cewa hayakin janareto ne ya kashe matan

- Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda na jihar, Wasiu Abiodun, da aka tuntube shi, ya tabbatar da lamarin amma bai bayar da sunayen matan ba

Rahotanni sun bayyana cewa akalla mata bakwai ne suka mutu a wani shagon kitso a karamar hukumar Rijau da ke jihar Nigeri.

Lamarin ya faru ne a ranar daren ranar Alhamis a lokacin da matan, da suka hada da matan aure guda biyu da 'yan mata biyar, suka je shagon kitson a shirye shiryen bukukuwan Sallah.

Har yanzu yanzu babu wani tabbaci na musabbabin mutuwarsu. Amma dai majiya a cikin garin ta shaida cewa hayakin janareto ne ya kashe matan.

Rahotanni sun bayyana cewa sakamakon ruwan da aka yi a yammacin ranar, ya sa matan suka yi haramar yin kitson Sallar.

Matar da ke da shagon kitson, ta shigar da janaraton a cikin shagonta, ta rufe kofar shagon tare da ci gaba da aikinta.

A dalilin hakan ne ake hasashen mata biyar suka mutu sakamakon shakar hayakin janareton, saboda rashin kofar da hayakin zai bi ya fita.

Rahotanni sun bayyana cewa sauran matan guda biyu sun tsira a wannan rana, amma a washe garin ranar ne suka ce "ga garinku".

KARANTA WANNAN: Fashewar karamin bam a harabar wani banki ya haddasa jikkatar mutane biyu

Bukukuwan Sallah: Yadda mata 7 suka mutu a gidan kitso
Bukukuwan Sallah: Yadda mata 7 suka mutu a gidan kitso
Asali: UGC

Sai dai, kokarin mutane na kai wadanda suka rayun zuwa asibitin Tungan Magajia ya samu tsaiko sakamakon wani babban dan siyasa na yankin da ya ce lallai sai shugagaban karamar hukumar, Bello Bako, ya ga gawar mutanen kafin a tafi da su.

Haka zalika rahotanni sun bayyana cewa bayan zanga zangar wasu mutane akan a hanzarta kai matan biyu asibiti, da kuma sa bakin Sarkin Rijau, Mohammed Gidiya, an kaisu asibiti.

Sai dai mintoci kadan suka mutu.

Gawarwakin matattun an mika su ga iyalansu, kuma an binne gawarsu kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

A cewar wata majiya, lamarin, ya jefa al'ummar Rijau cikin rudani da jimami a ranar Sallah, inda aka rinka yin gungu-gungu ana tattauna lamarin.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda na jihar, Wasiu Abiodun, da aka tuntube shi, ya tabbatar da lamarin amma bai bayar da sunayen matan ba.

Abiodun ya ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike kan musabbabbin mutuwarsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel