'Yan bindiga sun kashe mutum 14 a Kogi

'Yan bindiga sun kashe mutum 14 a Kogi

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane 14, ciki har da ‘yan gida daya mutum 13, a garin Agbudu da ke karamar hukumar Koton-Karfe ta jihar Kogi.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, mummunan ta'addanci ya auku ne da misalin karfe 2.00 na daren ranar Laraba, 29 ga watan Yuli.

Ede Ayuba, kwamishinan 'yan sanda na jihar, shi ne ya ba da tabbacin wannan rahoton yayin zantawa da manema labarai a Lakwaja, babban birnin jihar.

Kwamishinan ya ce ya yi gaggawar tura jami'an tsaro yankin da lamarin ya auku, sai dai an yi rashin sa'a tuni maharan sun cika bujensu da iska.

A yayin da ya jagoranci tawagar 'yan sanda wajen tsinto gawawwakin mutane 14 da suka afka cikin tarkon harin, kwamishinan ya ce an samu mutum 6 da suka jikkata.

Babban Sufeton 'Yan sandan Najeriya; Muhammad Adamu
Babban Sufeton 'Yan sandan Najeriya; Muhammad Adamu
Asali: Facebook

Ya ce babban takaici shi ne yadda harin ya ritsa da mutum 13 'yan gida daya wanda dukkaninsu sun riga mu gidan gaskiya.

"Mutum daya ne cikin 'yan gidan dayan da kwanansa ke gaba. Amma an kashe kawunsa, mahaifiyarsa, matar kawunsa, kaninsa, yayan matarsa, matarsa da kuma duk 'ya'yansa," inji kwamishinan 'yan sandan.

A wani rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito, Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Elkanemi, ya yi korafin cewa daga yanzu jihar Borno bata tsira ba.

Ya fadi hakan ne biyo bayan harin kwanan nan da aka kai wa ayarin motar Gwamna Babagana Zulum, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A ranar Laraba ne ‘yan ta’adda suka kai wa ayarin motocin gwamnan farmaki a garin Baga da ke karamar hukumar Kukawa na jihar yayin wata ziyara.

Da yake magana a lokacin gaisuwar Sallah da ya kai gidan gwamnati a Maiduguri, Shehu ya ce: “Ya mai girma, bamu ji dadin abunda ya faru ba a Baga, abun bakin ciki ne da kaico.

“Idan har za a iya kai wa ayarin motocin shugaban tsaro guda hari, toh wallahi, babu wanda ya tsira saboda shine mutum na daya a jihar.

“Idan har za a iya kai wa ayarin motocin irin wannan mutum mai daraja hari, to kuwa babu wanda ya tsira.

Lamarin na kara tabarbarewa, ina bukatar kowa da ya tashi mu hada hannu domin neman Allah ya shiga lamarin."

KARANTA KUMA: Shan shayi yana inganta lafiyar kwakwalwa - Bincike

Gwamna Zulum ya yi godiya ga Shehu a kan ziyarar sannan ya bashi tabbaci a kan shirin gwamnati na magance lamarin da ya gabatar.

Biyo bayan hare-haren kwanan nan da Boko Haram suka kai a jihar Borno da wanda aka kai kan ayarin motocin gwamnan, masu hasashe da manyan masu ruwa da tsaki sun yi kira ga sake lamarin tsaron kasar, ciki harda tsige shugabannin tsaron kasar.

Wani tsohon jigon rundunar soji na jihar Benue, Kanal Aminu Isa Kontagora (mai ritaya), ya kuma bukaci rundunar soji da ta binciki zargin Gwamna Babagana Zulum na cewa akwai masu barna da gangan cikin rundunar sojin.

KARANTA KUMA: Abinda ya kamata ku sani game da layin dogo mai amfani da lantarki da Ganduje zai gina a Kano

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng