Da duminsa: Uwar gidan shugaban kasar Brazil ta kamu da cutar COVID-19

Da duminsa: Uwar gidan shugaban kasar Brazil ta kamu da cutar COVID-19

Gwamnatin jihar Brazil a ranar Alhamis ta tabbatar da cewa uwar gidan shugaban kasar, Michelle Bolsonaro, ta kamu da cutar COVID-19 bayan shafe makonni biyu a killace da mijinta. Fadar shugaban kasar ta ce tana cikin koshin lafiya kuma a killace.

Uwar gidan shugaban kasar, Michelle Bolsonaro, ta kamu da cutar COVID-19 bayan shafe makonni biyu a killace da mijinta.

Sanarwar ta zo bayan kwanaki biyar da shugaban kasar Jair Bolsonaro ya ce ya warke daga cutar kuma ya dawo bakin aiki.

Michelle Bolsonaro, mai shekaru 38, "na cikin koshin lafiya kuma zata ci gaba da bin matakan kiwon lafiya," cewar wani jami'in fadar shugaban kasar.

"Uwar gidan na samun kulawa daga likitocin fadar shugaban kasa," a cewar jami'in.

Bolsonaro, mai shekaru 65, ya fuskanci kalubale kan yadda ya yi rikon sakainar kashi da cutar a Brazil, inda har kasar ta zamo ta biyu wajen masu dauke da cutar da kuma yawan mace mace.

Bayan kasar Amurka, kasar Brazil ce ta biyu da mutane sama da miliyan 2.5 da mace mace 90,000.

KARANTA WANNAN: Fashewar karamin bam a harabar wani banki ya haddasa jikkatar mutane biyu

Shugaban kasar wanda ya misalta cutar da 'mura', ya ki bin duk wasu matakai na kariya da nisantarwa a cikin kasarsa, yana mai cewa rushewar tattalin arziki ya fi illa akan cutar.

Da duminsa: Uwar gidan shugaban kasar Brazil ta kamu da cutar COVID-19
Da duminsa: Uwar gidan shugaban kasar Brazil ta kamu da cutar COVID-19
Asali: Twitter

Ya ce dage kan cewa sinadarin hydroxychloroquine na maganin cutar, kuma yayiwa kansa allurar sinadarin bayan kamuwa da cutar, duk da cewa ba a tabbatar da maganin ta ba.

Bolsonaro ya kasance ya na karya dokokin kariya daga kamuwa da cutar inda aka ga sau tari yana musaba ko rungume mabiyansa a wajen tarurruka.

Bayan da ya fara zazzabi, aka yi masa gwaji, aka tabbatar yana dauke da cutar a ranar 7 ga watan Yuli, ya yi makonni biyu a killace a fadar shugaban kasa, inda yake taro a yanar gizo.

Ministoci biyar na Bolsonaro sun kamu da cutar ta COVID-19. Na baya bayan nan shine na ranar Alhamis, inda ministan kimiyya da fasaha Marcos Pontes ya kamu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel