Fashewar karamin bam a harabar wani banki ya haddasa jikkatar mutane biyu

Fashewar karamin bam a harabar wani banki ya haddasa jikkatar mutane biyu

- Mutane biyu sun jikkata sakamakon fashewar karamin bam a harabar wani banki a jihar Oyo

- Fashewar bam din ya faru ne sakamakon wani fashi da makami da akayi a bankin, wanda ya tilasta kwamishin 'yan sanda zuwa harabar bankin

- Rundunar 'yan sandan ta ce hudu daga cikin 'yan fashin an cafke su kuma wasu fusatattu sun kona su

Akalla mutane biyu ne ake hasashen sun jikkata bayan da wani bam ya fashe a yayin ziyarar da kwamishinan 'yan sanda na jihar Oyo, Joe Enwonwu, ya kai wani bankin kasuwa.

Ya kai ziyara a bankin ne a garin Okeho, jihar Oyo. Daga cikin wadanda suka jikkata bayan fashewar, akwai jami'in 'yan sanda da kuma wani farar hula.

Rundunar 'yan sandan ta ce hudu daga cikin 'yan fashin an cafke su kuma wasu fusatattu sun kona su, yayin da rundunar ta samu nasarar cafke guda biyu.

Kakakin rundunar na jihar, Olugbenga Fadeyi, ya tabbatar da fashewar bam din ga manema labarai a ranar Alhamis.

A cewarsa, 'yan fashin a ranar Laraba sun bude kofar bankin ta hanyar harbi da bindiga kirar AK 47. Bayan sun shiga suka shiga wani daki suka yi awon gaba da kudade masu yawa.

Ya ce a lokacin da Mr Enwonwu ya ziyarci bankin a ranar Alhamis, an samu taruwar mutane cikin fusata, inda suka bukaci a basu 'yan fashin domin yanke masu hukunci.

KARANTA WANNAN: Karamin soja ya budewa babban soja wuta a jihar Borno

Fashewar karamin bam a harabar wani banki ya haddasa jikkatar mutane biyu
Fashewar karamin bam a harabar wani banki ya haddasa jikkatar mutane biyu
Asali: Twitter

Sai dai rundunar ba ta amince da bukatar mutanen ba, hakan ya sa jama'ar suka ki sauraron shugaban rundunar na matsawa nesa don samun damar yin bincike a wajen.

Karamin bam din da ya fashe ya jikkata jami'in rundunar da kuma wani farar hula daga cikin jama'ar wajen.

Haka zalika, Mr Fadeyi ya ce fusatattun sunyi kokarin kaiwa 'yan sandan farmaki amma Mr Enwonmu ya ba jami'an umurnin barin wajen don gudun tayar da hargitsi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng