Abinda ya kamata ku sani game da layin dogo mai amfani da lantarki da Ganduje zai gina a Kano

Abinda ya kamata ku sani game da layin dogo mai amfani da lantarki da Ganduje zai gina a Kano

Babban aikin shimfidar layin dogo na jirgin kasa mai amfani da lantarki wanda gwamnatin jihar Kano ke shirin aiwatar wa, cikin 'yan kwanakin nan ya zama abin kace-nace.

A yayin da wannan kudiri ke ci gaba da daukan hankali, babbar darikar siyasa ta Kwankwasiya, ta yi barazanar shiga kotu domin hana gwamnatin Kano karbo bashin kudaden da za a aiwatar da aiki daga kasar China.

Duk wannan tsegumi da 'yan hamayya ke yi, gwamnatin Kano yayin mayar da martani, ta ce ba ta da niyyar janye kudirin tunkarar kasar China domin ranto kudin da za ta aiwatar da wannan katafaren aiki.

Fadar gwamnatin ta ce babu irin sukar da za ta hana gwamnatin jihar aiwatar da manyan ayyuka domin mayar da jihar Kano katafaren birni da zai iya hada kafada da sauran manyan birane na kasashen duniya.

Hakan na zuwa ne bayan da gwamnatin Kano ta kammala tuntubar masu ruwa da tsaki, inda ta samu tabbaci cewa, wannan muhimmin aiki zai bunkasa harkokin kasuwanci a fadin jihar.

Gwamnan Kano; Abdullahi Umar Ganduje
Hoto daga fadar gwamnatin Kano
Gwamnan Kano; Abdullahi Umar Ganduje Hoto daga fadar gwamnatin Kano
Asali: Twitter

Gwamnatin Kano tana da yakinin cewa aikin baya ga fadada harkokin kasuwanci, zai kuma kawo saukin jigilar amfanin gona da sauran kayayyaki a tsakanin jihar wanda al'umma za su ci moriya mai dorewa.

Kamar yadda jaridar daily Trust ta ruwaito, a ranar 10 ga watan Oktoban 2016 ne majalisar dokokin jihar ta amince da dala 1,850,839,098 a matsayin jimillar kudin da aikin zai lakume.

Haka kuma amincewar gwamnatin tarayya ta biyo baya yayin da ta yi ruwa da tsaki wajen shigar da bukatar karbo bashin daga bankin mai suna China Export-Import Bank.

Tun a wancan lokaci, gwamnatin Kano ta kulla yarjejeniya da wani kamfanin gina layin dogo na kasar China, inda aka kiyasta cewa za a kammala rukunin farko da na biyu na kwangilar cikin shekaru hudu.

Bayan kulla yarjejeniyar kwangilar da kamfanin mai suna China Railway Construction Company, gwamnatin Kano ta kafa wani kwamiti da zai jibinci lamarin aikin karkashin jagorancin Alhaji Isiaku Umar Tofa.

KARANTA KUMA: N-Power: 'Yan Najeriya sun yi gangamin nuna godiya a fadar Aso Villa

Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya ce, yayin kammala aikin, ana sa ran shimfidar layin dogon za ta tafi tun daga Janguza zuwa Bata, Jogana zuwa Bata, Dawanau zuwa Bata da kuma daga Kwanar Dawaki-zuwa Bata.

Kwamishinan yada labarai na Kano, Muhammad Garba, ya ce bankin na China Export-Import Bank, shi ne zai dauki nauyin kashi 85 cikin dari na duk kudaden da kwangilar aikin za ta bukata kuma tuni ya amince da hakan.

A cewar kwamishinan, za a fara rukunin farko na aiki inda za a malala layin dogo tun daga kasuwar hatsi ta Dawanau har zuwa Bata cikin tsawon watanni ashirin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel