N-Power: 'Yan Najeriya sun yi gangamin nuna godiya a fadar Aso Villa

N-Power: 'Yan Najeriya sun yi gangamin nuna godiya a fadar Aso Villa

A ranar Laraba 29 ga watan Yuli, akalla 'yan Najeriya 2,000 sun yi tattaki tare da gudanar da gangamin nuna godiya har fadar shugaban kasa saboda da kyakkyawan tasirin da shirin N-Power ya yi a kasar.

Matasan wanda kungiyar 'yan kasa na gari (Concerned Citizen), ta jagoranta, sun gudanar da gangamin ne domin bayyana farin ciki da nuna godiyarsu ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Haka kuma matasan sun yi godiya ga ministar kula da agaji, bala'o'i da ci gaban al'umma, Hajiya Sadiya Umar Farouq, dangane da shirye-shirye na tallafi da rage radadin talauci da aka kirkiro domin 'yan kasa marasa galihu.

A jawabinsa, shugaban kungiyar ta 'yan kasa na gari, Ibrahim Kabiru Dallah, ya kwarara yabo da jinjina ga shugaban kasa Buhari a matsayin jagora wanda damuwa da halin da al'ummar Najeriya suke ciki ta mamaye zuciyarsa.

N-Power: 'Yan Najeriya sun yi gangamin nuna godiya a fadar Aso Villa
Hoto daga jaridar Leadership
N-Power: 'Yan Najeriya sun yi gangamin nuna godiya a fadar Aso Villa Hoto daga jaridar Leadership
Asali: Twitter

Kabiru Dallah ya ce shugaban kasa Buhari ba ya da wani mafificin buri face ganin ya samar da ci gaba mai dorewa a Najeriya.

Ya buga da misali da yadda gwamnatin shugaban Buhari ta dukufa wajen kawo shirye-shirye da dama na yaye talauci da ya yiwa al'ummar Najeriya katutu musamman marasa galihu.

A cewar kungiyar, gwamnatin Buhari ta yi kwazon a wannna fage tare da samun nasarori sakamakon jajircewa da fadin tashin da Hajiya Sadiya ta ke ci gaba da yi a matsayinta na wadda aka dora wa nauyin samar da ci gaban al'umma.

KARANTA KUMA: Wata kungiya ta tono tuggun tsige ministan shari'a na Najeriya

Kungiyar ta 'yan kasa na gari da kuma kungiyar masu cin moriyar shirin N-Power, sun shawarci ministar a kan kada ta yi kasa a gwiwa wajen yi wa kasar nan hidima tare da rike amanar aminci da kuma yarda da shugaba Buhari yake yi mata.

Da suke ci gaba da godiya, matasan sun ce a yayin da a halin yanzu gwamnatin shugaba Buhari ta ke shirin diban sabbin mutum 400,000 a rukuni na uku na matasan N-Power, suna fatan zuwa gaba adadin zai zarta haka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel