Tambuwal ya dora alhakin kalubalen ta'addancin da ya addabi Najeriya a kan rashin hadin guiwa

Tambuwal ya dora alhakin kalubalen ta'addancin da ya addabi Najeriya a kan rashin hadin guiwa

Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya fayyace dalilan da suka sanya ta'addancin 'yan daban daji yake ci gaba da ta'azzara a wasu sassa na kasar nan musamman yankin Arewa.

Tambuwal ya ce rashin hadin guiwa a tsakanin yankuna na daga cikin manyan dalilan da suka sanya Najeriya da kasashen da ke makwabtaka da ita suka gaza samun nasarar a fagen yaki da ta'addanci.

A cewarsa, Najeriya da makwabtan kasashe da suka hada da Chadi, Kamaru da Nijar, sun fada cikin tashe tashen hankula a 'yan shekarun da suka gabata.

Ya ce kasashen na ci gaba da gwagwarmayar magance barazanar kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram da kuma takwararta, ISWAP (Islamic State of West Africa).

Furucin hakan ya fito daga bakin gwamnan a yayin da ya ke gabatar da jawabansa ta yanar gizo a taron shekara-shekara kan sha'anin tsaro wanda Gidauniyar Umaru Shinkafi ta dauki nauyi.

Gwamnan jihar Sakkwato; Aminu Waziri Tambuwal
Gwamnan jihar Sakkwato; Aminu Waziri Tambuwal
Asali: Facebook

Gidauniyar mai suna Umaru Shimkafi Legacy Foundation, an gina ta ne domin tunawa da Marigayi Umaru Ali Shinkafi, tsohon Darakta Janar na kungiyar Tsaro ta kasa wadda a yanzu ta koma hukumar tsaro ta cikin gida (DSS).

Gwamnan ya ce a baya-bayan rundunar sojojin Najeriya tana fuskantar karancin dakaru da kuma karancin makamai da za su ribata domin tunkarar masu tayar da zaune a kasar nan.

Tambuwal ya kuma kira yi dukkanin hukumomin tsaro na kasar nan da hada kai wuri guda tare da hada karfi wajen magance matsalolin rashin tsaro da suka addabi al'umma a kasar.

Sai dai ya yaba da hadin kan da ake samu a tsakanin rundunar sojin kasa, na sama da kuma jami'an hukumar DSS da na 'yan sanda a jihar Sakkwato.

Ya ce akwai bukatar ayyukan jami'an tsaro ya zamana ana aiwatar da su a lokaci, amma muddin ba haka ba, za a rika samun ci gaban a fannin yaki da ta'addanci irin na 'mai hakar rijiya'.

KARANTA KUMA: PDP ta ɗage babban taron jam'iyya na jihohi huɗu

"A yayin da aka magance kalubale na rashin tsaro a Zamfara, Katsina, Neja ko Sakkwato, masu zaune tsayen za kuma su sauya sheka ne zuwa wasu jihohin."

Na yi magana da shugaban kasa a lokacin da na kai masa ziyara, a kan ya hada kai da shugaban kasar Nijar, domin akwai jihohi irinsu; Douso, Tahoua, Maradi da Zinder da ke iyaka da Najeriya, kuma duk suna fama da matsalolin 'yan daban daji.

"Sojojin Najeriya za su iya fattakar 'yan ta'adda zuwa Jamhuriyar Nijar, su ma kuma sojojin Jamhuriyar Nijar su fatattako su zuwa Najeriya wanda hakan zai sa a ga bayansu cikin lokaci takaitacce."

Sauran dattawan Arewa da suka halarci taron sun hadar da Gwamna Bello Matawalle na Zamfara, tsohon gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso, tsohon ministan tsaro, Abdulrahman Dambazau, tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari da sauransu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng