PDP ta ɗage babban taron jam'iyya na jihohi huɗu

PDP ta ɗage babban taron jam'iyya na jihohi huɗu

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya PDP, ta ɗage zaɓen fidda gwanayen takara da ta shirya gudanarwa a wasu jihohi huɗu na kasar har sai kuma mama ta gani.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, jihohin huɗu da jam'iyyar PDP ta ɗage babban taron da da za a gudanar zaɓen fidda gwanaye sun hadar da Ekiti, Neja, Sakkwato da kuma Taraba.

Hakan yana kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan ranar Litinin, 24 ga Yulin 2020, wadda jam'iyyar ta aike wa shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC.

Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus, da kuma babban sakataren jam'iyyar na kasa, Sanata Umar Tsauri, sun sanya a kan wasikar mai taken "ɗage zaɓen babban taron jam'iyya a jihohin Ekiti, Neja, Sakkwato da Taraba."

Shugaban PDP na kasa; Prince Uche Secondus
Shugaban PDP na kasa; Prince Uche Secondus
Asali: Facebook

A wasikar wadda hukumar INEC ta ba da tabbaci a kai, jam'iyyar PDP ba ta fayyace ainihin dalilan da suka sanya ta ɗage babban taron nata a jihohin hudu ba. Sai dai ta ce yanayi na ba zata ne ya janyo.

PDP ta bayyana cewa: "A kwafin wasiƙar mu mai lamba PDP/DOM CF. 2/VolIC/20-094, muna sanar da cewa yanayi na ba zata ya tilasta mana ɗage babban taron jam'iyya a jihohin hudu da abin ya shafa."

"Zuwa gaba ba da dadewa ba, za mu sanar da hukumar INEC da zarar an tsaida sabuwar rana."

KARANTA KUMA: Yaki da cin hanci da rashawa ya samar da kimanin $63.5b a cikin shekara guda - Malami

Ana iya tuna cewa, kusoshin jam'iyyar a jihohin hudu musamman a jihar Ekiti, sun shiga takun saka kan yadda ake tafiyar da tsarin jam'iyyar yayin da har ta kai ga an fara samun rabuwar kai.

A baya-bayan nan ne bangaren da ke goyon bayan tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yi nasara a gaban kotun a shari'arsu da bangaren Sanata Abiodun Olujimi mai wakiltar shiyyar Ekiti ta Yamma a majalisar dattawa.

Rahotanni sun bayyana cewa, ofishin jam'iyyar na kasa na kokarin ganin an yi sulhu a tsakanin fusatattun mambobin jam'iyyar a jihohin da abin ya shafa kafin a sanya ranar babban taron.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel