Yaki da cin hanci da rashawa ya samar da kimanin $63.5b a cikin shekara guda - Malami

Yaki da cin hanci da rashawa ya samar da kimanin $63.5b a cikin shekara guda - Malami

Lauyan koli kuma ministan shari'a na Najeriya, Abuabakar Malami, ya sanar da cewa kokarin da gwamnatin tarayya ta ke yi na yaki da cin hanci da rashawa, ya samar da kusan dala biliyan 63.5 a tsawon shekara guda.

A tsawon lokacin, Malami ya ce Ma'aikatar Shari'a wadda take karkashin jagorancinsa, ta tara wa kasar nan kimanin naira biliyan 2.1 da kuma dala miliyan dari takwas.

Ministan ya ce Ma'aikatar ta samu nasarar hakan ne a kimanin shari'o'i 80 na babbar kotun tarayya, manyan kotunan jiha da kuma Kotun Kungiyar raya tattalin arzikin Afrika ta Yamma wato ECOWAS.

Ministan Shari'a Abubakar Malami tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari
Ministan Shari'a Abubakar Malami tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari
Asali: Twitter

Lauyan kolin wanda ya bayar da cikakken bayani dangane da dukiyar da aka tara, ya kuma sanar cewa Najeriya tana tsammanin dala miliyan dari biyu daga kasar Holland da kuma Switzerland.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, sanarwa Malami ta zo ne a ranar Talata cikin birnin Abuja yayin gabatar da nasarorin da ma'aikatarsa ta samu tun daga ranar 29 ga Mayu, 2019 zuwa ranar 28 ga Yulin 2020.

Ministan ya ce nasarorin da aka samu a lokacin daga yaki da cin hanci ya hada da $ 62b da aka kwato a matsayin kudaden haraji daga kamfanonin mai; kusan $ 1b (daga OPL 245 - Malabu); $ 311m (daga Abacha loot III) da $ 6.3m (daga Abacha loot IV).

KARANTA KUMA: Bidiyon yadda karamin yaro ya ke yi wa mahaifiyarsa magiya yayin da take kokarin yi masa hukunci

Ministan ya ce nasarorin yaki da cin hanci da rashawa da aka samu a tsawon lokacin sun hadar da kudaden da aka kwato na dala biliyan 62 a matsayin basussukan haraji daga kamfanonin mai.

Sai kuma kimanin dala biliyan 1 daga rijiyoyin mai na OPL 245 da ke Malabu, da dala miliyan 311 na kudaden Abacha III da kuma dala miliyan 6.3 na kudaden Abacha IV.

Ya kara da cewa, kasar nan ta kuma tara Naira 685,784,757.09 daga tsarin nan na busa usur din fallasa masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati da kuma naira miliyan 500 ta hanyar gwanjon kadarorin da gwamnatin ta kwace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel