Mpeni Kofi: Bishiya mai shekaru 300 da ake zargin tana komawa mutum tsakar dare

Mpeni Kofi: Bishiya mai shekaru 300 da ake zargin tana komawa mutum tsakar dare

- Wata bishiya a kasar Ghana mai suna Mpeni Kofi ana zargin tana komawa mutum don bai wa jama'a kariya

- An gano cewa bishiyar ta kai shekaru 300 a duniya kuma ita ce ke gadin jama'ar Akuapem a cikin dare

- Legit.ng ta duba tsohon tarihin bishiyar mai cike da al'ajabi da bada mamaki wacce take tun zamanin kaka da kakanni

Wata bishiya mai suna Mpeni Kofi a kasar Ghana mai shekaru 300 a duniya, ana zargin tana komawa dogon mutum dan Adam don bai wa jama'ar yankin kariya.

Har a yanzu saiwoyin bishiyar na nan kuma ganyayyakinta koraye duk da karni 30 da ta kwashe a duniya. Wasu jama'ar yankin na bautar bishiyar kamar yadda kaka da kakanninsu ke yi.

Jama'ar Akuapem na zargin cewa bishiyar ce ke basu kariya, Ghanaweb ta ruwaito.

Legit.ng ta gano cewa mukaddashin shugaban Akuapem, Nana Addo Kwataa da mataimakinsa, Ahenenanhene Osae Adade, sun bayyana cewa bishiyar na da wasu alamu na mutuntaka.

Bishiyar da aka rufe da farin launi ta kasan ta, magabatansu na cewa ta taba karesu daga harin yaki da aka kai musu.

A yayin tuna tarihin jama'ar Akuapem, Nana Addo Kwataa ya ce suna ganin Mpeni Kofi a matsayin wani abu na musamman da ke shiryar da su.

Kamar yadda yace: "Alamu ne garemu, za mu iya bibiyarta har mu isa gida a yayin da muka bace yayin yaki.

"A shekaru 300 da suka gabata tun zamanin kakanninmu, an ce tana da matukar amfani don suna bauta mata. Har yau muna bauta mata."

Ahenenanhene Osae Adade, ya zarga cewa a duk lokacin da suka kwanta bacci, Mpeni Kofi na zagayawa garin a siffar dogon mutum don basu kariya.

Mpeni Kofi: Bishiya mai shekaru 300 da ake zargin tana komawa mutum tsakar dare
Mpeni Kofi: Bishiya mai shekaru 300 da ake zargin tana komawa mutum tsakar dare. Hoto daga Britanica
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun damke 'Kasko', gagarumin dan bindiga daga Nijar

Shugabannin sun yarda cewa bishiyar na da wata babbar alaka ta musamman da fadar Okuaphene kuma ita ke hada kawunan jama'ar da ke gidajen da ke zagaye da ita.

A wani labari na daban, shugaba bature daya aka taba yi a kasar Zambia kuma sunansa Peter Fisher, wanda aka sani da Chief Nyamwana.

Ya jagoranci kabilar yankin Mwinilunga da ke Zambia.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng