Bidiyon yadda karamin yaro ya ke yi wa mahaifiyarsa magiya yayin da take kokarin yi masa hukunci

Bidiyon yadda karamin yaro ya ke yi wa mahaifiyarsa magiya yayin da take kokarin yi masa hukunci

Wani bidiyo wanda a baya bayan nan ya bayyana a yanar gizo, ya nuna yadda wani karamin yaro ya durƙusa ya na roƙon afuwar mahaifiyarsa bayan ya yi mata laifi.

A cikin faifan bidiyon, ƙaramin yaron yana ta rusa kuka yana roƙon mahaifiyarsa ta 'kwantar da hankalinta ya ɗan huta kaɗan' kafin ɗaukar wani mataki a kansa.

Bayan ya dauki tsawon wani lokaci ya na roƙon ba tare da ta nuna alamar za ta hakura ba, sai yaron ya durƙusa ya ci gaba da neman sasancin mahaifiyarsa, duk don ya tsira daga hukuncin da take shirin yi masa.

Ita kuwa mahaifiyar yaron ta yi tsaye ke kam, tare da nanata masa cewa sai fa ta yi masa dukan tsiya duk da wannan magiya da yake yi mata.

Bidiyon karamin yaro da mahaifiyarsa ke kokarin lakada wa duka ya karade zauren sada zumunta
Bidiyon karamin yaro da mahaifiyarsa ke kokarin lakada wa duka ya karade zauren sada zumunta
Asali: Instagram

Sai dai kuma faifan bidiyon ya yanke ba tare da sanin mai ya faru a karshe ba, walau ta hukunta shi ko kuma ta hakura.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumuntar zamani na Florence Wathoni Anyansi, daya daga cikin masu shirin gidan BBNaija na wannan shekarar nan ya bai wa jama'a da yawa mamaki.

Budurwar ta bayyana yadda ta samu juna biyu duk da kuwa da budurcinta kuma bata taba lalata da kowa ba a lokacin da take shekaru 23.

A bidiyon da a halin yanzu ya karade kafafen sada zumuntar zamani, mahaifiyar yaro dayan ta bayyana cewa ta samu dan wani lokaci tare da saurayinta suna shafe-shafen juna.

KARANTA KUMA: Badakalar da ta mamaye hukumar NDDC laifin gwamnatin da ta gabata ne - Lai Mohammed

Daga nan ne ya goga mazakutarsa a gabanta har ya fitar da maniyyi duk da kuwa bai shiga ko ina ba.

Wathoni ta ce bayan aukuwar lamarin ta daina ganin al'adarta amma bata dauka al'amarin da muhimmanci ba saboda ta san ba zai yuwu ta samu ciki ba bayan basu yi wani abun a zo a gani ba.

'Yar shekaru 29 a halin yanzu, ta bayyana cewa ta gano tana dauke da juna biyu ne bayan watanni biyar da aukuwar lamarin sakamakon gwaje-gwajen da tayi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel