Kotu ta bada umurnin cafke tsohon magatakardan majalisar tarayya, Sani Omolori

Kotu ta bada umurnin cafke tsohon magatakardan majalisar tarayya, Sani Omolori

- Babbar kotun FCT, Maitama, Abuja ta bayar da umurnin cafke tsohon maganatarkan majalisar tarayya, Mohammed Omolori

- Hukumar EFCC ce ta bukaci kotun data bada umurnin cafke Mr Omolori

- EFCC ta ce akwai alakar Mr Omolori da binciken da take yi na karkatar da motoci 27 da kudinsu ya kai miliyan dari hudu

Mai shari'a Suleman Belgore na babbar kotun FCT, Maitama, Abuja a ranar Litinin, ya bayar da umurnin cafke tsohon maganatarkan majalisar tarayya, Mohammed Omolori.

Mr Belgore ya bayar da umurnin ne biyo bayan wata kara da hukumar EFCC ta shigar a kotunsa inda ta bukaci kotun ta bada umurnin cafke Omolori.

Hukumar EFCC a cikin takardar bukatar mai dauke da lamba M/8728/2020, da ta gabatar gaban kotun, ta yi zargin cewa wanda take karar ya ki amsa gayyatarsa da suka yi domin binciken da suke gudanarwa game da wani zargi da ake masa.

EFCC ta ce tana binciken wata badakala ne, na karkatar da motoci 14 kirar Hilux da kuma kirar Peugeot 508 guda 13, da kudinsu ya kai miliyan dari hudu.

A cewar hukumar, daga cikin binciken, ta gayyaci sakataren hukumar majalisar tarayya, Adamu Fila, Mr Oluseye Ajakaye da wasu masu mukamai a hukumar.

Ta kara bayyana cewa wadanda suka gayyata sun amsa, kuma sun alakanta Mr Omolori da tuhumar, amma bai amsa gayyatar hukumar ba duk da wasikun da ta aika masa a ranar 4 ga watan Nuwamba, 2019.

EFCC ta kara da cewa ta aika masa wata wasikar a ranar 16 ga watan Maris, 2020, nan ma ya yi biris da gayyatar.

KARANTA WANNAN: Yan Nigeria da aka tura karatu kasar waje sun koma kamar almajirai a UK - Dabiri

Kotu ta bada umurnin cafke tsohon magatakardan majalisar tarayya, Sani Omolori
Kotu ta bada umurnin cafke tsohon magatakardan majalisar tarayya, Sani Omolori
Asali: Twitter

A kan hakan, EFCC ta garzaya kotun domin nuna bukatarta na a bada umurnin cafke Mr Omolori.

Bayan sauraron koken hukumar EFCC, mai shari'a Belgore ya bayar da wannan umurni.

A wani labarin kuma; shugabar hukumar da ke kula da 'yan Nigeria mazauna kasashen waje (NIDCOM), Mrs Abike Dabiri-Erewa ta bayyana cewa akwai dalibai da ke karatu a Burtaniya da suka koma tamkar almajirai.

Komawarsu kamar almajirai a cewarta ya faru ne sakamakon nuna halin ko in kula da masu daukar nauyin karatunsu suka nuna akansu.

Da wannan ta roki mai daukar nauyin karatun daliban, hukumar bunkasa yankin Niger Delta (NDDC) da ta hanzarta turawa daliban kudadensu, da kudaden makaranta da sauransu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel