Yan Nigeria da aka tura karatu kasar waje sun koma kamar almajirai a UK - Dabiri

Yan Nigeria da aka tura karatu kasar waje sun koma kamar almajirai a UK - Dabiri

- Hukumar NIDCOM ta bayyana cewa akwai dalibai da ke karatu a Burtaniya da suka koma tamkar almajirai

- Hukumar ta yi kira ga ministan bunkasa Niger Delta, Sanata Godswill Akpabio da ta gaggauta biyan alawus da kudaden karatun daliban

- A halin da ake ciki dai, daliban sun dade suna kiraye kiraye da a waiwayesu sakamakon halin da suke ciki na rashin kudi

Shugabar hukumar da ke kula da 'yan Nigeria mazauna kasashen waje (NIDCOM), Mrs Abike Dabiri-Erewa ta bayyana cewa akwai dalibai da ke karatu a Burtaniya da suka koma tamkar almajirai.

Komawarsu kamar almajirai a cewarta ya faru ne sakamakon nuna halin ko in kula da masu daukar nauyin karatunsu suka nuna akansu.

Da wannan ta roki mai daukar nauyin karatun daliban, hukumar bunkasa yankin Niger Delta (NDDC) da ta hanzarta turawa daliban kudadensu, da kudaden makaranta da sauransu.

Ta ce hakan ne kawai zai ba daliban damar ci gaba da karatunsu a kasar.

A cikin wata sanarwa a ranar Talata, NIDCOM ta yi waiwaye kan wata wasika ga ministan ma'aikatar Niger Delta Godswill Akpabio da aka tura masa a ranar 18 ga watan Yuni, 2020.

Wasikar mai taken NIDC/001/20/1, ta yi kira ga ministan kan batun kudin jirgin jigilar daliban, tare da bukatar NDDC da ta biya kudin saboda ita ce ta dauki nauyin karatun daliban.

KARANTA WANNAN: Yiwa yar shekaru 6 fyade: Kotu ta yanke wa wani mutumi daurin rai-da-rai

Yan Nigeria da aka tura karatu kasar waje sun koma kamar almajirai a UK - Dabiri
Yan Nigeria da aka tura karatu kasar waje sun koma kamar almajirai a UK - Dabiri
Asali: Twitter

Ya kara da cewa hukumar ta dogara ne da tabbacin ministan na cewar zai biya dukkanin alawus alawus na daliban da kudaden karatunsu.

A halin da ake ciki dai, daliban sun dade suna kiraye kiraye da a waiwayesu sakamakon halin da suke ciki na rashin kudi.

A wani labarin; wata babbar kotun jihar Ekiti da ke da zama a Ado-Ekiti a ranar Litinin ta yankewa Ishau Gruma hukuncin daurin rai-da-rai bayan kamashi da laifin yiwa 'yar shekara 6 fyade.

Wanda aka yiwa hukuncin, Ishau Gruma, ya aikata laifin ne a ranar 20 ga watan Yuli 2019, a Erio-Ekiti, karanar hukumar Ekiti ta Yamma.

Mai shari'a A.A Adeleye na babbar kotun jihar ta 5 ne ya yanke hukuncin bayan samunsa da laifin yiwa yarinyar fyade, duk da cewa ya musanta zargin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel