Sojin Najeriya sun damke 'Kasko', gagarumin dan bindiga daga Nijar

Sojin Najeriya sun damke 'Kasko', gagarumin dan bindiga daga Nijar

Hedkwatar tsaro ta kasa ta ce rundunar soji ta Operation Sahel Sanity ta yi nasarar halakawa tare da kama 'yan bindiga masu tarin yawa, masu satar shanu, masu garkuwa da mutane da sauran 'yan ta'adda a yankin arewa maso yamma.

Mukaddasin daraktan yada labarai na hedkwatar tsaron, Birgediya janar Benard Onyeuko, ya bayyana hakan ne a wata takardar da ya fitar a ranar Litinin a garin Abuja.

Onyeuko ya bayyana cewa, rundunar a ranar 22 ga watan Yuli ta yi nasarar damke shahararren mai siyar da makamai mai suna Musa Abubakar wanda aka fi sani da Kasko ko Buzu daga kauyen Mai Wake a yankin Dakoro da ya Maradin jamhuriyar Nijar.

Ya ce an kama wanda ake zargin ne a farfajiyar wata makaranta a Gusau inda 'yan uwansa ke aikin gadi.

Kamar yadda yace, wanda ake zargin ya saba samar wa 'yan bindiga makamai daga jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya ta kananan hukumomin Sabon Birni da Isah na jihar Sokoto.

"A halin yanzu, wanda ake zargin yana hannunmu kuma yana samar da bayanai masu amfani ga rundunar.

"Hakazalika, a ranar 25 ga watan Yuli, rundunar da aka tura karamar hukumar Sabuwa ta samu kiran gaggawa a kan garkuwa da mutane da ake yi a garin.

"A gaggauce rundunar ta garzaya yankin inda bayan fatattakar miyagun da tayi, suka tsere tare da barin mutum hudu da suka sace.

"An mika mutum hudun ga 'yan uwansu," yace.

Sojin Najeriya sun damke 'Kasko', gagarumin dan bindiga daga Nijar
Sojin Najeriya sun damke 'Kasko', gagarumin dan bindiga daga Nijar. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bidiyo: Yadda na samu ciki da budurcina duk da ban taba jima'i da kowa ba - Budurwa

Onyeuko ya kara bayyana cewa, a ranar 25 ga watan Yulin, rundunar ta kashe 'yan bindiga biyu bayan samamen da ta kai Gurbin Baure bayan bayanan sirri da ta samu.

Ya kara da cewa, sauran 'yan bindigar ukun da suka tarar sun kama su, kuma a halin yanzu suna hannun rundunar.

Kamar yadda yace, rundunar da aka tura Bena ta kama wani mutum mai suna Garba Faduwa da ke kai wa 'yan bindigar bayani a Anguwan Yara, Bankami, Faduwa da Danlayi a jihar Zamfara.

"Wanda ake zargin a halin yanzu yana fuskantar tuhuma. A ranar dai, rundunar sojin da ke sintiri a kauyen Dan Kadai sun ci karo da 'yan bindiga a kauyen Akawo da ke karamar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara.

"Yan bindigar sun tsere tare da barin wani mutum daya da suke garkuwa da shi mai suna Alhaji Lawal Mamman.

“An ceto mutumin tare da raunata wasu daga cikin 'yan bindigar kafin su tsere.

“Shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanal janar Tukur Buratai ya jinjinwa rundunar a kokarinta da jajajircewarta.

"Ya yi kira garesu da kada su sare wurin tabbatar da nasara," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel