Lakcarori, ma'aikatan gwamnatin tarayya da na jiha na zambatar aikin N-Power

Lakcarori, ma'aikatan gwamnatin tarayya da na jiha na zambatar aikin N-Power

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, akwai wasu malaman manyan makarantun gaba da sakandire da ma'aikatan gwamnatin tarayya da na kuma jiha da ke zambatar shirin N-Power.

An ruwaito cewa akwai wasu ma'aikatan gwamnati da ke cin moriyar shirin N-Power cikin rukunin farko da na biyu na matasan da aka diba alhali su na daukan albashi a wasu wuraren aikin na daban.

Makasudin shirin N-Power wanda aka kirkiro tun a shekarar 2016, gwamnatin tarayya ta samar da shi domin daukar matasa marasa aiki da suka kammala karatu, kuma aka sanya musu alawus na N30,000 duk wata.

A yanzu an samu wasu daga cikin matasan da aka diba a rukunin farko da na biyu da suke zambatar shirin duk da kuwa suna aiki a wasu ma'aikatu na gwamnati da suke samun albashi mai tsoka.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan shi ne ya ke nuna irin rashin ingantaccen tsarin gudanar da sha'anin daukan aiki da biyan albashin ma'aikata a kasar.

Ministar kula da ayyukan jin kai, bala'o'i da ci gaban al'umma; Sadiya Umar Farouq
Ministar kula da ayyukan jin kai, bala'o'i da ci gaban al'umma; Sadiya Umar Farouq
Asali: UGC

Hakan kuma yana ci gaba da faruwa duk da tsarin biyan albashin bai-daya na IPPIS da gwamnati ta assasa da manufar dakile duk wata kafa ta rashin gaskiya da ta danganci daukan aiki da biyan albashin ma'aikata.

Sai dai a binciken da jaridar Vanguard ta gudanar, ta gano cewa akwai wasu da ke cin moriyar shirin N-Power da gan-gan kuma su yi biris wajen karbe albashi a wasu ma'aikatun gwamnati.

Wata majiya ta ba da shaidar cewa, akwai wani dan uwanta da ke cin moriyar shirin N-Power alhali kuwa yana karbar albashi a matsayinsa na lakcara a jami'ar Calabar.

Majiyar wadda ita ma tana cin moriyar shirin ta ce dan uwan nata bayan kasancewarsa malamin jami'a, ya kuma ci gaba da karbar alawus dinsa na shirin N-Power cikin matasan da aka diba tun a rukunin farko.

A ranar Alhamis ta makon da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta bayar da shaidar cewa, tabbas akwai wasu matasa masu zambatar shirin N-Power alhalin su na aiki a wasu ma'aikatun na gwamnati.

KARANTA KUMA: Ma'aurata sun azabtar da yaron gida kan ƙosan N100

Dalilin hakan ya sanya ma'aikatar kula da ayyukan jin kai, bala'o'i da ci gaban al'umma, ta sanar da cewa, an dakatar da biyan alawus na wasu masu cin moriyar shirin N-Power 14,020.

Cikin wata sanarwa Rhoda Iliya, mataimakiyar darektan labarai ta ma'aikatar ta fitar, ta ce ba za a biya wasu masu amfanar shirin N-Power alawus ba saboda an gano suna karbar albashi a wasu ma'aikatun na gwamnati.

Ta ce ofishin Akanta Janar na kasa na kokarin ganin an warware matsalar sauke nauyin bashin alawus din watannin baya ga masu cin moriyar shirin na N-Power da suka cancanta.

Don haka Ministar ma'aikatar, Sadiya Umar Farouq, ta ke ba da hakuri a kan jinkirin da tantance masu cin moriyar shirin N-Power na hakika ya haddasa.

Ta ce babu shakka da zarar ofishin Akanta Janar na kasa ya kammala warware matsalar, za a saki alawus din ga wadanda suka cancanta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel