Ma'aurata sun azabtar da yaron gida kan ƙosan N100
Jami'an tsaro na hedikwatar 'yan sanda da ke garin Orji a jihar Imo, sun cafke wasu ma'aurata; Goodluck Ogbuji da matarsa; Benita kan zargin aikata laifin cin zarafin dan Adam.
Mijin da matarsa sun shiga hannu sakamakon azabtar da Wisdom, wani yaron gidansu wanda bai wuce shekaru takwas ba a duniya kan ƙosan Naira 100.
Wasu ma'aikatan jarida biyu; Chidiebube Okeoma da Harriet Ijeomo, su ne suka yi wa ma'aurantan biyu cunen jami'an tsaro har gidansu a Unguwar Umudagu Mbieri da ke karamar hukumar Mbaitoli ta jihar.
Ana zargin magidantan biyu sun gallazawa yaron nasu azabar tsiya saboda kawai ya sayo ƙosan Naira 100 a maimakon na Naira 50.

Asali: Twitter
Okeoma ya ce, "Mun samu labarin cewa ma'auratan sun ci zarafin yaron gidan nasu da har suka kusa su kashe shi saboda ya sayo ƙosan Naira 100 a maimakon na Naira 50."
"Mun yi bincike ta hanyar zaurukan sada zumunta kuma muka sami adireshin gidansu."
"Jami'an 'yan sanda sun yi wa gidan dirar mikiya tun da duku-dukun ranar Alhamis, inda suka cafke azzaluman ma'auratan tare da ceto yaron gidan."
"A yanzu haka suna tsare a ofishin 'yan sanda na Orji yayin da jami'ai ke ci gaba da kula da yaron."
"Girman raunukan da suka gadar wa yaron ya nuna mafi kololuwar zalunci. Muna neman a bi masa hakkinsa."
KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta warewa 'yan siyasa kashi 10% na guraben kananan ma'aikata 774,000 da za ta dauka
"Muna son a gurfanar da ma'aurantar a gaban kuliya domin a zartar musu da hukunci kwatankwacin laifin da suka aikata."
A ofishin 'yan sandan, Uwargijiyar yaron, ta amsa laifinta da cewa sharrin Shedan ne kuma a yanzu tana cizon yatsa.
Sai dai kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, Orlando Ikeokwu, ya ce za su yi dukkanin abinda ya dace wajen tattaro hujjojin gurfanar da ma'aratan biyu a gaban alkali.
Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, tun a shekarar 2019 ne Wisdom ya daina zuwa makaranta domin yi wa ma'auratan bauta.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng