Alkawarin shekaru 30: Aboki ya raba $22m da ya ci wurin caca da abokinsa

Alkawarin shekaru 30: Aboki ya raba $22m da ya ci wurin caca da abokinsa

Wani abokin amana ya cika alkawarin da ya dauka na shekaru 30 a watan Yunin 2020. Ya yanke hukuncin raba kudin da ya samu wurin cacarsa har dala biliyan 22 da babban abokinsa bayan da suka yi wannan alkawarin shekaru 30 da suka gabata.

A 1992, manyan abokan juna, Thomas Cook da Joseph Feeney sun dauka alkawarin raba duk abinda suka samu a wurin caca daidai da juna matukar daya daga ciki ya ci.

Basu rubuta yarjejeniyar a takarda ba amma sun hada hannu bayan alkawarin, jaridar The Nation ta ruwaito.

A watan Yunin 2020, shekaru masu tarin yawa bayan wannan alkawarin, Thomas Cook da ke Elk Mound ya yi nasarar cin cacar bayan siyan tikitin da yayi a wani wurin siyar da gas da ke Menomonie.

Bayan nasarar, Cook ya tuntubi abokinsa Joseph Feeney. Da farko Feeney yana zargin Cook wasa yake saboda kowanne mako sai sun siya tikitin cacar amma babu sa'a.

Dukkan su sun amince da adana dala biliyan 16.7 sannan za su samu wasu dala 5.7 na harajin jihar da tarayya. Dukkansu sun yi murabus daga aiki kuma suna shirin zuwa hutu ne.

Alkawarin shekaru 30: Aboki ya raba $22m da ya ci wurin caca da abokinsa
Alkawarin shekaru 30: Aboki ya raba $22m da ya ci wurin caca da abokinsa. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda matashi ya shiga sata amma ya kare da yi wa tsohuwa fyade

Sun ce suna da burin kashe kudin nan tare da juna amma za su kwashi yaransu da jikoki don zuwa hutu.

"Tabbas za mu iya abinda mukeso da kudin," Cook yace.

Cook ya bai wa wurin siyar da gas din da ya siya tikitin kyautar dala 100,000 kyauta.

A wani labari na daban, wani wanda ake zargin dan kungiyar asiri ne mai shekaru 20 mai suna Somtochukwu Onyebuchi, ya bayyana cewa ya ja kananan yara biyar zuwa kungiyar asirin a jihar Anambra.

Wanda ake zargin, mai aski ne a kauyen Ire da ke Ogidi, karamar hukumar Idemili ta jihar. Yana daga cikin wandanda ake zargi 103 da rundunar 'yan sandan ta damke.

Ya dora laifin a kan shaidan tare da jan kunnen wadanda har yanzu ke cikin kungiyar da su fice, The Nation ta ruwaito.

Ya ce: "Na kasance dan kungiyar asiri ta JVC tun a 2015 kuma na ja kananan yara biyar ciki. Na san hanyar jan hankalin kananan yaran.

"Na yi nadamar shiga wannan harkar saboda ba zan ce ga abinda na karu da shi ba tun bayan shigata kungiyar. Ina shawartar sauran 'yan kungiyar da su tuba kafin a kama su."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel