Da duminsa: FG ta sanar da sabuwar ranar fara WASSCE
A ranar Litinin, gwamnatin tarayya ta bukaci dukkan makarantun sakandire da ke fadin kasar nan da su bude don dalibai da ke ajin karshe su kammala. Za a bude makarantun ne a ranar 4 ga watan Augusta.
An sanar da cewa, za a fara jarabawar kammala sakandire wacce hukumar shirya jarabawa ta yammacin Afrika ke shiryawa farawa a ranar 17 ga watan Augusta.
Wannan na kunshe ne a wata takarda da daraktan yada labarai da hulda da jama'a na ma'aikatar ilimi, Ben Goong ya sa hannu.
Gwamnatin tarayya (FG) ta sanar da cewa za a bude makarantun sakandire a fadin kasa domin bawa daliban da ke shekarar karshe damar zana jarrabawar kammala karatun sakandire (WASSCE).
A cikin wata sanarwa da ma'aikatar ilimi ta fitar a yau, Litinin, ta bayyana cewa za a bude makarantun ne daga ranar Talata, 4 ga watan Agusta, 2020.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Ben Bem Goong, darektan yada labarai na ma'aikatar ilimi ta kasa.
A cewar sanarwar, an yanke shawarar bude makarantun ne bayan masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi sun shafe lokaci mai tsawo suna tattaunawa a ranar Litinin.
Daliban da ke aji shidda; watau shekarar karshe, da takwarorinsu da ke aji uku ne kawai zasu koma makaranta, a cewar sanarwar.

Asali: Twitter
KU KARANTA: Korar Sanusi II daga Kano da tsaresa: IGP ya bukaci kotu da ta yi watsi da karar
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Ben Bem Goong, darektan yada labarai na ma'aikatar ilimi ta kasa.
A cewar sanarwar, an yanke shawarar bude makarantun ne bayan masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi sun shafe lokaci mai tsawo suna tattaunawa a ranar Litinin.
Daliban da ke aji shidda; watau shekarar karshe, da takwarorinsu da ke aji uku ne kawai zasu koma makaranta, a cewar sanarwar.
"Za a bude makarantn sakandire daga ranar 4 ga watan Agusta, 2020, ga daliban ajuzuwan da zasu rubuta jarrabawar kammala makaranta. Hakan zai bawa dalibai damar yin amfani da sati biyu domin yin shirin jarrabawar WAEC, wacce za a fara ranar 17 ga watan Agusta," a cewar sanarwar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng