Boko Haram: Buratai ya ziyarci sojin Najeriya da ke jinya a Kaduna (Hotuna)
Shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai, a ranar Lahadi ya ziyarci sojojin da ke jinya a asibitin sojoji na 44 da ke jihar Kaduna.

Asali: Twitter
Babban hafsin sojan, ya dauka alkawarin tabbatar da walwalarsu tare da yi musu fatan samun lafiya da gaggawa.

Asali: Twitter
Da yawa daga cikin dakarun sojin da ke jinyar wadanda suka samu raunika ne sakamakon yaki da Boko Haram da kuma 'yan bindiga a yankin arewacin Najeriya ne.

Asali: Twitter
A yayin ziyarar, shugaban sojin ya ci abincin rana tare da majinyatan sojin sannan da kanshi ya dinga zuba musu abinci.

Asali: Twitter
Buratai ya tabbatar da cewa yaki da ta'addanci alhakin kowa ne kuma ya tabbatar da cewa walwalar dakarun abin dubawa ce.

Asali: Twitter
Ya ce za su tabbatar da cewa kowannensu ya samu lafiya sannan da ingantacciyar kulawa.

Asali: Twitter
Ya kara da cewa, duk da kalubalen da suke fuskanta wurin yaki da ta'addanci da suka hada da raunika da mutuwa, rundunar sojin ta shirya kawo karshen ta'addanci da sauran laifuka.

Asali: Twitter
A bangarensu, wasu daga cikin sojojin sun nuna jin dadinsu a kan ziyarar da shugaban rundunar sojin ya kai musu. Sun nuna shirinsu na komawa bakin fama idan sun warke.

Asali: Twitter
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng