Rundunar 'yan sanda ta kori jami'anta hudu saboda laifin cin amanar kasa

Rundunar 'yan sanda ta kori jami'anta hudu saboda laifin cin amanar kasa

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kwara, ta kori jami'anta hudu bayan ta same su da laifin rashin gaskiya da cin amanar wani da ake zargi.

Haka zalika an hukunta wasu jami'an takwas bayan an same su da laifuka daban-daban na cin amanar aikinsu.

A cewar kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Peter Okasanmi, jami'an hudu da aka sallama daga aiki an same su ne da aikata wasu manyan laifuka.

Okasanmi ya ce, kwamishinan ‘yan sanda na jihar ya ba da umarnin sake shari'ar daya daga cikin jami’an hudu da aka kora daga aiki.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, kakakin 'yan sandan ya ce "daya daga cikin jami'an hudu an sake bitar shari'arsa kuma aka tabbatar da hukuncin kora daga aiki a kansa."

'Yan sandan Najeriya
Hoto daga jaridar Premium Times
'Yan sandan Najeriya Hoto daga jaridar Premium Times
Asali: Twitter

Cikin jami'an hudu da aka sallama daga aiki, an ba da sunayen biyu daga cikinsu sakamakon laifin da suka aikata na tatsar dukiyar wani mutum da ya shiga hannunsu da suka yi.

Sanarwar ta ce, "Sajen Sola Akano da Kofura Babatunde Glorious, sun yi kwacen naira miliyan 1,190,000 a hannu wani mutum da ake zargi da laifi."

"Basu tsaya iya nan ba, sun kuma tayar da jijiyar wuya a kan sai 'yan uwan mutumin sun biya naira dubu dari 200 kafin a yi belinsa."

"Jami'an 'yan sandan biyu sun kuma karbe wayoyin salula guda biyu a hannun mutumin yayin da suka kama shi, inda suka mayar da su domin amfanin kansu."

An bankado wannnan badakala ne bayan da mutumin ya shaki iskar 'yanci, kuma aka shigar da korafi har gaban hukumomin da suka dace.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta tsawaita wa'adin neman aikin N-Power zuwa mako biyu

Ba ya ga Akano da Glorious, kakakin 'yan sandan bai fayyace sunayen ragowar jami'an biyu da aka kora daga aiki ba.

Haka kuma bai fadi laifukan da sauran jami'an takwas suka aikata da kuma hukuncin da aka dauka a kansu.

Sau tari dai an sha kama jami'an 'yan sandan Najeriya suna aikata ba daidai musamman a lokutan da na'urar daukan hoton biyo ta hasko su suna tsaka ta tatsare a hannun mutanen da ake zargi da laifi ko kuma masu ababen hawa.

Wasu daga cikin jami'an da aka kama da irin wannan miyagun laifuka, tuni an kore su daga aiki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel