'Dan kasuwa ya mutu a hannun 'yan sanda bayan kwanaki 6 ba tare da an gurfanar da shi a kotu ba

'Dan kasuwa ya mutu a hannun 'yan sanda bayan kwanaki 6 ba tare da an gurfanar da shi a kotu ba

Wani dan kasuwa ya riga mu gidan gaskiya bayan ya shafe kwanaki shida ya na tsare bai ko rintsa ba a hannun jami'an tsaro na 'yan sanda.

Kehinde Omotosho na kasuwar Gbagi da ke birnin Ibadan a jihar Oyo, ya yi gamo da ajali a hannun reshen binciken miyagun laifuka na hukumar 'yan sandan jiha.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, Mista Omotosho mai shekaru 45, yana daya daga cikin wasu mutanen da rundunar 'yan sanda ta dasa wa wawa da misalin karfe 12.00 na daren ranar 16 ga watan Yuli.

Jami'an tsaro sun shigo yankin na Agugu a sukwane domin cafke wani dan uwan Omotosho, Kabir, wanda ake zargi da hannu a cikin wata rigima da har ta kai ga salwantar ran wani mutum a yankin.

Jami'an 'yan sanda
Hoto daga jaridar Premium Times
Jami'an 'yan sanda Hoto daga jaridar Premium Times
Asali: Twitter

An ci gaba da tsare Omotosho a dakin da ake ajiyar masu laifi na ofishin 'yan sandan har na tsawon kwanaki 6, wanda hakan ya saba wa awanni 48 da dokar Najeriya ta shar'anta na tsare duk wanda ake tuhuma.

A cewar daya daga cikin wadanda aka kama, Jelili Rasak, ya ce Omotosho ya mutu ne a dakin ajiyar masu laifi a ranar 21 ga watan Yuli sakamakon azabtarwa.

Ya ce "Omotosho ya kasa bacci kuma suna tsaye kikam babu dare babu rana a dan tsukukun dakin. A daren ranar Litinin bayan kwanaki hudu da kama mu, rashin lafiya mai tsanani ta kama Omotosho."

"Da misalin karfe 5.00 na safiyar ranar Talata 21 ga watan Yuli, Omotosho ya ce ga garinku nan a dakin ajiye masu laifi," inji Rasak

Jaridar ta ruwaito cewa, "a madadin a bai wa Omotosho damar samun kulawar mahukuntan lafiya, 'yan sandan sun ɗaure shi da igiyoyi kuma suka kwantar da shi yana fuskantar kasa har wayewar gari."

KARANTA KUMA: Hukumar NEDC ta raba wa tubabbun 'yan Boko Haram kayan tallafi

Rasak ya ce kafin mai yankan kauna ta cimma Omotosho, ya rika tsandara ihu yana neman a kawo masa ɗauki amma jami'an suka yi burus da shi.

"Sai da sauran fursunonin suma suka fara ihu sannan aka kai Omotosho asibiti, inda a nan ya cika."

A yayin tuntubar kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Olugbenga Fadeyi, ya musanta cewa Omotosho ya mutu ne a dakin ajiye masu laifin.

Fadeyi ya ce "Omotosho ya kamu da rashin lafiya a dakin ajiye masu laifi kuma aka mika shi asibitin 'yan sanda inda a nan ya cika. An kuma sanar da 'yan uwansa dangane da lamarin."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel