Hukumar NEDC ta raba wa tubabbun 'yan Boko Haram kayan tallafi

Hukumar NEDC ta raba wa tubabbun 'yan Boko Haram kayan tallafi

A karshen makon da ya gabata ne aka yi bikin yaye tsofaffin 'yan Boko Haram 601 da suka tuba a jihar Gombe kamar yadda hedikwatar tsaro ta kasa DHQ ta ba da sanarwa.

Tubabbun 'yan Boko Haram sun yi wa gwamnatin Najeriya rantsuwar ba zasu kara tsoma kansu a harkar kowane nau'i na ta'addanci ba. An mai da su cikin al'umma.

Babban jami'in kula da Operation Safe Corridor, Bamidele Shafa, ya ce an yaye tubabbun 'yan Boko Haram din bayan an ba su kyakkyawan horo na gyara halayya da saisaita musu tunani da cire musu akidar ta'addanci a zukatansu.

An yi bikin yaye tsoffin 'yan ta'addan ne a ranar asabar bayan an basu horo na tsawon watanni shida a sansanin zare akidar ta'addanci da gyara hali na Malam Sidi da ke karamar hukumar Kwami ta Jihar Gombe.

Tubabbun 'yan Boko Haram
Hoto daga jaridar Premium Times
Tubabbun 'yan Boko Haram Hoto daga jaridar Premium Times
Asali: UGC

Hakan ya faru ne bayan kwanaki kadan da wasu mazauna jihar Borno suka nuna rashin amincewarsu da komawar tubabbun 'yan Boko Haram cikin al'umma domin ci gaba da rayuwa.

A shekarar 2016 ne rundunar dakarun tsaro ta Najeriya ta kaddamar da Operation Safe Corridor, wani shiri na gyara halin da saisaita tunani gami da zare akidar ta'addanci ga tsofaffin 'yan Boko Haram da suka tuba.

A cewar Bamidele, cikin tubabbun 'yan ta'addan da aka yaye akwai 14 'yan kasar Kamaru, Chadi da kuma Nijar.

KARANTA KUMA: Saudiya ta gindaya sabbin sharuda takwas ga masu aikin Hajjin bana

Yayin bikin, Hukumar farfado da ci gaban yankin Arewa maso Gabas, NEDC, ta yi wa tubabbun 'yan Boko Haram din goma ta arziki inda ta rarraba musu kayayyakin tallafi domin su samu abin dogaro na tsayuwa da kafarsu.

Shugaban hukumar Malam Abba Musa, shi ne ya gabatar da kayayyakin tallafin ga tsoffin 'yan ta'adda yayin komawarsu cikin al'umma kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.

Daga cikin kayayyakin da aka rarraba musu sun hadar da; injinunan walda 130, kayan aikin kafinta 20, kayan aski da janareta 111, kekunan dinki 105, kayan hada takalma 95 da sauransu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel